Tsarin kasa: Dole fa a sake lale a Najeriya-Inji Jam’iyyar PDP

Tsarin kasa: Dole fa a sake lale a Najeriya-Inji Jam’iyyar PDP

– Shugaban PDP Ahmed Makarfi yace dole a zauna game da tsarin Najeriya

– Jam’iyyar adawar na gani cewa fa dole sai an yi tsarin kasar garambawul

– Makarfi yake cewa ba lalama za a shawo kan duk matsalolin kasar nan

Ahmed Makarfi ya nemi a zauna game da tsarin kasar nan. Wasu dai na nema su balle daga Najeriya a halin yanzu. Sanata Makarfi yace don haka ne ake bukatar a zauna.

Tsarin kasa: Dole fa a sake lale a Najeriya-Inji Jam’iyyar PDP

Babu abin da sulhu ba zai yi magani ba Inji Ahmed Makarfi

Jam’iyyar PDP mai adawa ta nemi a zauna game da tsarin Najeriya. Yanzu haka wasu dai na nema su balle daga Najeriya inda wasu kuma ke ganin ya kamata a bar masu kasar su. Don haka ne Jam’iyyar ke gani sai an zauna.

KU KARANTA: Allah yayi wa Danmasanin Kano rasuwa

Shugaban bangaren PDP Sanata Ahmed Makarfi yace lokaci yayi fa da dole a zauna domin duba tsarin Najeriya. Makarfi yace ko ba jima ko ba dade sai an zauna da kowa domin samun maslaha a kasar.

Ku na da labari cewa bangaren Ahmed Makarfi dai na Jam’iyyar PDP yayi Allah-wadai da tafiyar Nnamdi Kanu. Makarfi ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin Channels.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

'Yan Najeriya sun fara tambayar Ina Buhari?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel