Matasa sun ba shugaba Buhari wa’adin makonni 8 ya yi murabus

Matasa sun ba shugaba Buhari wa’adin makonni 8 ya yi murabus

- Wata kungiya mai suna Nigerian Youth Advocate for Justice sun yi barazanar jagorantar matasa miliyan bakwai don tsige shugaban kasa Buhari ta tsiya idan har yaki yin murabus cikin makonni 8

- Shugaban kungiyar, Seriki Olorunwa, ya ce halin rashin cikakken lafiya da shugaban kasa ke fama da shi ya hana shi samun damar shugabantar kasar

- Matasan sun bayyana cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta na wulakanta ‘yan Najeriya saboda ayyukan son kanta

Wata kungiyar matasan Najeriya mai suna the Nigerian Youth Advocate for Justice sun ba shugaban kasa Muhammadu Buhari wa’adin makonni takwas ko ya yi murabus ko kuma ya kafa gwamnatin wucin-gadi sakamakon rashin sa a kasar na tsawon kwanaki 53.

Kungiyar ta yi gargadin cewa idan shugaban kasa ya ki ba da hadin kai ga wa’adin, zai yi sanadiyar da matasa miliyan bakwai zasu tsige shi a jihohi 22, jaridar Guardian ta ruwaito.

Shugban kungiyar, Seriki Olorunwa ya ce halin da shugaban kasar ke ciki na rashin lafiya ya hana sa damar gudanar da gwamnatin kasar.

KU KARANTA KUMA: YANZU YANZU: Allah ya yi ma tsohon ministan Najeriya Maitama Sule rasuwa

Ko da yake matasan sun sha alwashin cewa bazasu zubar ko wani jinni ba, amma sun bayyana cewa a shirye suke suyi yaki maimakon rayuwa a matsayin bayi.

Kungiyar sun bayyana cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta na wulakanta ‘yan Najeriya saboda ayyukan son kanta.

Matasan sunyi korafin cewa kashe-kashe, sace-sacen mutane da fashi ya zamo ruwan dare a Najeriyar da muke a yanzu.

A halin da ake ciki, jam’iyyar APC ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari na samun sauki sosai daga rashin lafiyarsa sabanin cewa da akayi bai san inda kansa yake ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyo na NAIJ.com don jinra'ayin jama'a a kan shugaban kasa Muhammadu Buhari:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel