YANZU YANZU: Allah ya yi ma tsohon ministan Najeriya Maitama Sule rasuwa

YANZU YANZU: Allah ya yi ma tsohon ministan Najeriya Maitama Sule rasuwa

- Allah ya yi ma sanannen shugaban nan na arewa kuma tsohon ministan Najeriya Alhaji Maitama Sule rasuwa

- Ya kasance dan takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar National Party of Nigeria amma ya sha kaye inda Shehu Shagari ya yi nasara

Allah ya yi ma tsohon ministan tarayyan Najeriya, Alhaji Maitama Sule rasuwa.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa Alhaji Sule ya rasu a wani asibitin Cairo, dake kasar Masar a safiyar yau a cewar wata majiya ta kusa da marigayin.

NAIJ.com ta tattaro cewa Yusuf Maitama Sule ya kasance dan siyasar Najeriya. A shekarar 1976, ya zamo kwamishinan sauraron kukan jama’a na tarayya, matsayin da ya zamar da shi jagaba a kasar.

KU KARANTA KUMA: PDP ta kalubalanci Buhari da ya yi murabus, kamar yadda ya shawarci Yar’Adua a 2009

YANZU YANZU: Allah ya yi ma tsohon ministan Najeriya Maitama Sule rasuwa

Allah ya yi ma tsohon ministan Najeriya Maitama Sule rasuwa

A farkon shekarar 1979, ya tsaya takarar shugabancin kasa karkashin jam’iyyar National Party of Najeriya amma ya sha kaye a hannun Shehu Shagari.

Bayan sake zaben shugaban kasa Shagari a 1983, an nada Maitama Sule a matsayin Ministan dake jagorantar kasar, wanda aka shirya domin taimaka wa shugaban kasar gurin yaki da rashawa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyo na NAIJ.com a kasa:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel