PDP ta kalubalanci Buhari da ya yi murabus, kamar yadda ya shawarci Yar’Adua a 2009

PDP ta kalubalanci Buhari da ya yi murabus, kamar yadda ya shawarci Yar’Adua a 2009

- Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa akwai tarin cututtuka daban-daban sannan kum Buhari ya yi abun da ya kamata, idan gaskiya ne cewan ba lallai ya samu lafiya ba

- Jam’iyyar ta bayyana cewa kamar yadda ake bukatar ko wani ma’aikacin gwamnati, ‘yan Najeriya na sa ran shugaban kasar ya kasance cikin koshin lafiya sannan kuma a kan aiki

- Jam’iyyar ta tunatar da shugaban kasar kana bun da ya fadi da bakin shi, cewa bait aba irin wannan rashin lafiyar ba a baya

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) babin Akwa Ibom ta kalubalanci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya zamo mai gaskiya a kan rashin lafiyarsa.

A wani hira da jaridar Daily Sun, sakataren labarai na jam’iyyar PDP babin jihar Akwa Ibom, Ini Ememobong ya fada ma Buhari da ya dubi girma da arziki ya yi murabus idan har rashin lafiyarsa ba zai bari ya gudanar da aikin sa a matsayin shugaban kasar Najeriya ba.

KU KARANTA KUMA: Gowon ya bukaci ‘yan Najeriya da su rungumi zaman lafiya

Jam’iyyar ta bayyana cewa Buhari ya bukaci hakan daga marigayi shugaban kasa Umar Musa Yar’Adua a shekarar 2009 lokacin da ya kamu da rashin lafiya.

A halin yanzu, NAIJ.com ta rahoto a baya cewa uwargidan shugaban kasa, Aisha Muhammadu Buhari ta bar Abuja don ziyartan mijinta dake jinyan mijinta a Landan.

A wata sanarwa daga Suleiman Haruna, Daraktan bayanai ga uwargidan shugaban kasar, ya bayyana hakan a ranar Lahadi, 2 ga watan Yuli.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel