Gowon ya bukaci ‘yan Najeriya da su rungumi zaman lafiya

Gowon ya bukaci ‘yan Najeriya da su rungumi zaman lafiya

- Tsohon shugaban kasa, Yakubu Gowon, ya roki ‘yan Najeriya da su hadu suyi addu’a don samun lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Gowon ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su yi ma mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo addu’a da ma dukkanin shugabanni na kasar

- Tsohon shugaban kasar ya ce addu’a na maganin matsaloli cikin sauri fiye da sojoji, haka kuma fiye da makamin yaki

Tsohon shugaban kasa, janar Yakubu Gowon ya bukaci ‘yan Najeriya da su guje ma duk wani tashin hankali, ayyukan ta’addanci da kuma hali da ka iya raba kasar.

Ya yi wannan kira ne a ranar Lahadi, 2 ga watan Yuli, a Sokoto a gurin taron addu’a na kwana daya da kungiyar addu’o’in Najeriya ta shirya, kamfanin dillancin labarai (NAN) ta ruwaito.

“Mu mutunta rayukan mutane irinmu da Allah ya hallita don wata manufa. Karda mu dauki rayuka da rashin hukunci.

KU KARANTA KUMA: Aisha Buhari ta koma Landan don sake duba lafiyar shugaban kasa

“Muna gudanar da addu’a kan cewa karda ‘yan Najeriya su kuma daga hannayensu a tsakaninsu.

“Su so junansu duk da ban-bancin addini, ra’ayi, siyasa da kabilanci,” ya kara da cewa.

Gowon, ya roki ‘yan Najeriya da su hadu suyi ma shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’an samun lafiya.

Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su yi ma mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo addu’a da ma dukkanin shugabanni na kasar

Tsohon shugaban kasar ya yabi gwamnan jihar Sokoto kan gudunmuwarsa, da kuma karamcinsa da tabbatar da an cimma gangamin.

Madugun shirya taron, Bishop Godwin Okafor, ya ce an shirya gangamin ne domin rokon dorewar zaman lafiya, hadin kai da kwanciyar hankali a Najeriya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel