Aisha Buhari ta koma Landan don sake duba lafiyar shugaban kasa

Aisha Buhari ta koma Landan don sake duba lafiyar shugaban kasa

- Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ta koma Landan don ta sake duba lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Matan shugaban kasar ta ce zata isar da sakkonin fatan alheri da kuma addu’o’in da ‘yan Najeriya ke yiwa mijinta

- Ana sa ran Hajiya Aisha Buhari zata biya a Addis Ababa don ta halarci taron matan shugabanin Afrika kafin ta ci gaba zuwa Landan a ranar Talata

Uwargidan shugaban kasar, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari, a ranar Lahadi, 2 ga watan Yuli ta bar Najeriya zuwa Landan don ta sake duba lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ke hutun duba lafiyarsa a Birtaniya.

Wata sanarwa dauke da sanya hannun daraktan bayanai na Malama Aisha Buhari, Suleiman Haruna ya ce uwargidan shugaban kasar zata ziyarci shugaba Buhari kuma zata isar da sakonnin fatan alheri da kuma addu’o’in da ‘yan Najeriya ke yiwa shugaban kasar.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, sanarwar ta kara bayyana cewa, ana sa ran Hajiya Aisha Buhari zata biya a Addis Ababa babban birnin kasar Ethopia don ta halarci taron kungiyar matan shugabanin Afrika wato Organization of African First Ladies against HIV / AIDS (OAFLA), wanda za a yi yau 3 ga watan Yuli.

Aisha Buhari ta koma Landan don sake duba lafiyar shugaban kasa

Uwargidan shugaban kasar, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ta koma Landan

KU KARANTA: Har yanzu ba a rasa na kwarai: Abin da wata Ma’aikaciyar Gwamnati tayi ya bada mamaki

“Uwargidan shugaban kasar zata ci gaba da tafiyarta zuwa Landan a ranar Talata, 4 ga watan Yuli, 2017". A cewar sanarwar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel