Rikici a Masarauta: Rikita rikita a fadar Sarkin Musulmi tayi ƙamari, ta ɗauki sabon salo

Rikici a Masarauta: Rikita rikita a fadar Sarkin Musulmi tayi ƙamari, ta ɗauki sabon salo

Takaddama da taki ci, taki cinyewa tsakanin magajin garin Sakkwato, Alhaji Danbaba da Magatakarda babba na jihar Sakkwato, kuma mataimakin shugaban jam’iyyar APC, Abdulkadir Inuwa, kamar yadda NAIJ.com ta ruwaito.

Sakamakon wannan rikici ne ya sanya Danbaba yin murabus daga sarautarsa, inda yayi zargin mai alfarma Sarkin Musulmi na yunkurin tafka kuskure ta hanyar nada Inuwa sarautar Marafan Sakkwato, sakamakon iyayensa bayi ne, a cewar Danbaba.

KU KARANTA: Rikici tsakanin jikan Sardauna da jigon APC tayi fallatsa har fadar Sarkin Musulmi

Sai dai a wani sabon salo da rikicin ta dauka, Danbaba ya shaida ma jaridar Daily Trust cewa don kashin kansa yayi murabus da sarautar magajin gari, inda ya musanta labarin wai an tilasta mai murabus ne.

Danbaba yace bai taba rokon Sarkin Musulmi ya tsaya masa ba wai da sunan EFCC na bincikensa, inda yace ba shi da matsalar ko sule da EFCC, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito.

Rikici a Masarauta: Rikita rikita a fadar Sarkin Musulmi ta ɗauki sabon salo

Sultan da Danbaba

“Idan ba taba rokonsa ya shige min gaba a wata matsala da nake da shi da EFCC, toh ya bari, ya dakata, bani bukatar taimakonsa daga yau. Don me zasu je suna yayata ni wai inada matsala da EFCC? Lamarin da ya faru tun a watan Janairu.” Inji shi

Danbaba yace batun EFCC da ake fadi shine kamfaninsa Bina Consult tayi aiki ma kungiyar gwamnonin Najeriya a shekarar data gabata, kuma EFCC ta gayyaci dukkanin wadana lamarin ya shafa tun a watan Janairu.

“Da kaina nayi murabus, na mayar musu da Qur’anin da suka bani, da motar da aka bani, idan kuma sun ce su suka sallame ni, toh ina takardar Sallamar?” Inji Danbaba

Daga bisani, Danbaba yace kiyayyar dake tsakanin Sardauna da kakan Sultan ne yake neman tasowa, kuma ke neman ya shafe shi, yace “Idan baka manta ba, babansa ya daure Kakana, wannan shine tushen rikicin dake nema ya shafe ni.”

Rikici a Masarauta: Rikita rikita a fadar Sarkin Musulmi ta ɗauki sabon salo

Inuwa

Daga karshe Danbaba yace “Ai Sultan ne ya umarci Inuwa ya kai ni kotu, ta yaya za’ayi mutumin dake son a gurfanar dani gaban kotu kuma yace zai yi mana sulhu? Kawai su je, bani bukatar komai daga wajensu.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin Najeriya kasa daya ce? Kalla

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel