Zan hukunta duk wanda ya furta kalaman kiyayya a jihar na – Inji wani Gwamna arewa

Zan hukunta duk wanda ya furta kalaman kiyayya a jihar na – Inji wani Gwamna arewa

- Gwamnan jihar Nasarawa ya lashi takobi cewa zai hukunta duk wanda aka kama da furta kalaman kiyaya a jihar

- Gwamnan ya gargadi sarakunan gargajiya da su ja kunni masu irin wannan furucin ko su sanar da jami’an tsaro

- Al-Makura ya ce zai yi wa kowa adalci a jihar a matsayin su na ‘yan kasar

Gwamna Umaru Tanko Al-Makura na Jihar Nasarawa, ya yi alkawarin hukunta duk wani mutum ko kungiya wanda aka kama da furta kalaman kiyaya a jihar.

Al-Makura ya yi wannan gargadi ne a ranar Lahadi, 2 ga watan Yuli a lokacin da sarakunan gargajiya, a karkashin jagorancin Sarkin Lafia, Alhaji Isah Mustapha Agwai, suka ziyarce shi a fadan gwamnatin jihar wanda ke Lafia domin taya shi murnar dawowa daga humura.

Al-Makura ya ce wadanda ke amfani da siyasa inda suke furta wasu kalaman kiyaya don zuga mutane, gwamnati zata dauka matakan tabbatar da cewa irin wannan furcin bai jawo tashin hankali tsakanin al’umman jihar ba.

Zan hukunta duk wanda ya furta kalaman kiyayya a jihar na – Inji wani Gwamna arewa

Gwamna Umaru Tanko Al-Makura na Jihar Nasarawa

KU KARANTA: Wani na-kusa da Goodluck Jonathan ya fice daga PDP

NAIJ.com ta ruwaito cewa, gwamnan ya bukaci sarakunan gargajiya da su gargadi duk masu hannu a cikin irin wannan kalaman kuma su sanar da jami'an tsaro idan suka ki kulawa da su.

Gwamna Al-Makura ya yi alkawari cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kare hakkin 'yan kasa da kuma tabbatar da cewa za a yiwa kowa da kowa adalci a jihar a matsayin su na 'yan kasar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel