Yaron kirki: Matashi ɗan Najeriya ya mayar ma gwamnati albashinsa na watanni 2

Yaron kirki: Matashi ɗan Najeriya ya mayar ma gwamnati albashinsa na watanni 2

- Mataimakin shugaban kasa ya jinjina ma wani matashi dan Najeriya

- Farfesa Yemi Osinbajo ya yaba ma yaron ne sakamakon gaskiyarsa

Mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana godiyarsa tare da jinjina ma wani matashi dan Najeriya sakamakon halin gaskiya da rikon amana da ya nuna.

Shi dan wannan matashi mai suna Daniel Joshua ya fito ne daga jihar Taraba, inda yake daya daga cikin matasan dake amfana da tsarin gwamnati na tallafa ma matasa, N-POWER.

KU KARANTA: Jakadun ƙasashen Turai sun yi hawan Sallah a Kano, kalli hoton a nan

A karkashin tsarin N-POWER ana biyan mutanen dake cin gajiyarsa N30,000 a duk wata bayan sun danyi wasu aikace aikace a makarantu, asibitoci da gonaki.

Yaron kirki: Matashi ɗan Najeriya ya mayar ma gwamnati albashinsa na watanni 2

Yaron kirki: Daniel Joshua

Ana cikin haka ne, sai Daniel ya samu aiki a watan Afrilu, inda ya rabu da aikin N-POWER, amma duk da haka sai ya samu albashin watannin Afrilu da Mayu, sai dai Daniel bai cinye kudaden ba, inda ya mayar dasu asusun gwamnati.

NAIJ.com ta ruwaito mukaddashin shugaban kasa Osinbajo yana yaba ma Daniel, inda yace “Baya da samun aikin da yayi, Daniel ya nuna shi mutum ne mai amana.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Hanyoyin kare kai daga masassara:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel