Dansanda ya kiɗime, ya harbi kansa, yayi ƙoƙarin bindige kwamishinan Yansanda

Dansanda ya kiɗime, ya harbi kansa, yayi ƙoƙarin bindige kwamishinan Yansanda

- Ɗansanda yayi barazanar harbe kwamishinan Yansanda, ya buɗe wuta

- Hakan ya faru ne a ofishin yansanda dake jihar Legas

Wani dansanda mai mukamin Inspeka dake runduna ta 20 na Yansandan MOPOL, Ikeja jihar Legas ya rikirkice inda yayi yunkurin bindige kwamishinan Yansandan jihar Legas.

Dansandan mai suna Inspekta Magaji ya tafi shelkwatar ofishin kula da adashin gata na Yansanda ne sanye da kayan gida, inda ya bukaci ya gana da kwamishinan Yansanda mai kula da wannan sashi.

KU KARANTA: Yawan Musulmai a birnin Sydney na ƙasar Australia ya haura 253,435

Sai dai wani Dansanda mai suna Pius Oguche ya bukaci ya san dalilin dayasa Magaji ke son ganin Kwamishiniyar, daga nan ne fa Magaji ya zaro bindiga yayi barazanar harbe Pius, muddin ya tsare masa gaba, inji rahoton The Sun.

Dansanda ya kiɗime, ya harbi kansa, yayi ƙoƙarin bindige kwamishinan Yansanda

Dansanda

Sai dai Inspekta Pius yayi ta maza inda ya cije lallai ba zai barsa ya shiga ofishin Kwamishiniyar Yansandan ba, inda Inspekta Magaji ya fita hayyacinsa yana barazanar harbe duk dansandan dake wajen, hakan ya sanya manyan hafsan Yansanda ranta ana kare.

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito, yayin da ake cikin wannan kacaniya ne sai wani dansanda ya harbo Magaji daga nesa a kafa, kan kace me, shi kuwa Magaji ya fara harbin mai kan uwa da wabi, inda ya kara harbin kafarsa.

Daga karshe dai an ci karfinsa, inda aka garzaya da shi asibiti, tare da fara gudanar da bincike akan sa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin dansanda abokin kane? kalla

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel