Nnamdi Kanu ya raina mana hankali Inji wasu Inyamurai

Nnamdi Kanu ya raina mana hankali Inji wasu Inyamurai

– Wasu Inyamurai a waje sun yi watsi da Nnamdi Kanu

– Kungiyar Inyanmuran su kace ba da bakin su yake magana ba

– Su kace Nnamdi Kabn bai isa yayi magana a madadin kowa ba

Wasu Inyamurai na cewa Nnamdi Kanu ba da bakin mu yake magana ba. Inyamuran da ke wajen kasar nan ne su ka bayyana hakan kwanan nan. A cewar su babu wanda ya zabi Kanu yayi magana a madadin wasu.

Nnamdi Kanu ya raina mana hankali Inji wasu Inyamurai

Nnamdi Kanu ba da bakin mu yake magana ba Inji wasu Inyamurai

Wasu Inyamurai da ke kasar waje sun yi kaca-kaca da Jagoran Biyafara Nnamdi Kanu su kace bai isa yayi magana da yawun su ba. Inyamuran su kace babu wanda ya sa ko ya isa yayi magana da bakin Inyamuran Duniya.

KU KARANTA: Wani Gwamna ya tsige Kwamishinonin sa

Nnamdi Kanu ya raina mana hankali Inji wasu Inyamurai

Nnamdi Kanu bai isa ka ari bakin mu ka ci mana albasa ba

Inyamuran da ke Kasar Afrika ta Kudu karkashin Shugaban Cif Jonas Udeji ya nesanta kan sa daga Nnamdi Kanu wanda yake kokarin ganin Yankin Kudu ya zama kasa mai cin gashin kan ta ko ta wani irin hali.

Kun ji cewa Shugaban Sarakunan Kasar Ibo Cif Eze Cletus yace su na nan a Arewacin Najeriya. Sarkin ya bayyana abin da ya sa ba za su bar Yankin ba amma kuma ya kara da cewa a nemi a zauna lafiya.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko za a kara samun hadin kai a Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel