Baza mu iya dena karban cin hanci ba - Yan sandan Anambra

Baza mu iya dena karban cin hanci ba - Yan sandan Anambra

-Mun gwamace mu karbi cin hanci domin shugabanin mu suna kawo mana cikas cikin bincike

-Bamu mu da isasun wajen ajiye masu laifi a jihar Anambra

-Mafi yawancin mazauna garin masu laifi ne

A yayin da babban sifeton yan sanda na kasa ke kokarin kawo sauyi a cikin aikin yan sandan, musamman hana karban cin hanci da kame ba bisa ka’ida ba, wasu yan sanda da ke aiki a jihar Anambra sunce su dai ba za su iya dena karban cin hanci ba.

Kafar yadda labarai na P.M. Express ta bada rahoto cewa yan sandan sun ce babu wanda zai hana su tsare masu abin hawa domin bincike a titunnan jihar saboda yadda yananyin jihar Anambran yake.

Su dai wadannan yan sandan sun ce dalilin da yasa baza su dena karban ‘kudin goron’ ba shine mafi yawancin mazauna garin masu laifi ne wanda zasu iya aikata komi akan duk wani dan sanda da ke kokakrin tabbatar da an bi doka.

Baza mu iya dena karban cin hanci ba - Yan sandan Anambra

Baza mu iya dena karban cin hanci ba - Yan sandan Anambra

Sun kuma yi ikirarin cewa, idan sun kama mai laifi sun fara bincike domin yin hukunci kamar yadda doka ta tanadar, kawai sai suji umarni daga shugabanin su cewa a saki wanda ake tuhuma da laifin komin girman abin da ake tuhumar sa dashi.

Soboda haka yafi mana sauki mu karbi cin hanci, da zaman dirshan kawai” inji wani jami’in yan sandan.

KU KARANTA: Uwar bari: Senata Dino Melaye ya fara neman sauki

P.M. Express ta ziyarci jihar kuma ta lura cewa mafi yawancin lungunna da hanyoyin na garin zaka tadda yan sanda suna tare masu abin hawa suna karban cin hanci, kawai dai suna cin Karen su babu babbaka.

Idan dai kana amfani da abin hawa kuma ka kadu da yan sanda, abin da yafi sauki kawai shine ka basu kudi kayi tafiyar ka” Inji wani mai mota.

Har ila yau, kafar yadda labaran ta ruwaito cewa idan jami’an yan sandan zasu yi aikin su kamar yadda doka ta tanadar, mazauna garin da yawa zasu tsinci kansu a gidan maza saboda laifufunka da suke aikatawa. Amma bamu samun goyon baya daga sama kuma bamu da wuraren da zamu ajiye masu laifin.

Hanyoyin da aka hangi yan sandan suna tare masu abin hawa sun hada da hanyar Onitsha, Awka, nnewi, Ekwulobia, Oko, Uga, Umunze, Abagana, Mahadar Aromo, Agulu, Uke, Awkuzu da dai sauran su.

Kakorin ji ta bakin jami’in hulda da jama’a na yan sandan bai yiwu ba domin wayoyin sa a kasha suke.

Wata majiya tace wannan ba sabon abu bane a jihar kuma duk wani kwamishina da yayi kokarin kawo sauyi ba zai samu nasara ba domin jami’an yan sandan baza su bashi hadin kai ba.

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel