Ana zaune kalau: Gwamna Fayose ya kora gaba daya Kwamishinonin sa

Ana zaune kalau: Gwamna Fayose ya kora gaba daya Kwamishinonin sa

– Gwamnan Jihar Ekiti Ayo Fayose ya sallami dukka Kwamishinonin sa

– Ayo Fayose ya gode masu da irin bautar da su kayi wa Jihar

– Gwanan ya nemi su mika takardun aiki ga Sakatarorin su

Gwamna Ayodele Fayose ya kora duk Kwamishinonin sa Hakan na zuwa ne bayan Gwamnan Ribas Wike yayi haka. Ba a dai san dalilin wannan babban zazzaga haka ba.

Ana zaune kalau: Gwamna Fayose ya kora gaba daya Kwamishinonin sa

Ayo Fayose ya sallami Kwamishinonin sa

Mai girma Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Peter Fayose ya kora duk Kwamishinonin sa kamar yadda mu ka samu rahoto. Mai taimakawa Gwamnan wajen yada labarai ta kafafen zamani Lere Olayinka ya bayyana haka.

KU KARANTA: Jam'iyyar PDP ta soki tafiyar Nnamdi Kanu

Ana zaune kalau: Gwamna Fayose ya kora gaba daya Kwamishinonin sa

Gwamna Fayose ya sallami kaf Kwamishinonin sa

Olayinka ya bayyana cewa Gwamnan ya jinjinawa irin kokarin da wadannan Bayin Allah su kayi wa Jihar ya kuma umarce su da su mika duk takardun aiki ga Sakatarorin su na din-din-din. Kwanan nan ne Gwamna Wike shi ma yayi irin wannan zazzaga.

Ku na da labari kwanaki Gwamna Ayodele Fayose yace Shugaba Buhari yana can bai san inda yake ba. Gwamnan yace Shugaban kasar na cikin wani irin wani hali wanda bai iya ko numfashi. Tuni dai aka karyata wannan kalamai na Gwamnan.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

'Yan Najeriya sun fara neman Shugaban kasar su

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC
NAIJ.com
Mailfire view pixel