An daura Ahmed Musa da Sahibar sa Juliet a Garin su

An daura Ahmed Musa da Sahibar sa Juliet a Garin su

– An yi daurin gargajiyan Dan wasa Ahmed Musa da Juliet

– Manyan ‘Yan wasan Najeriya sun halarci wannan biki

– Daga ciki akwai ‘Dan wasa Raheem Lawal na Super Eagles

Jiya ‘Yan wasan Super Eagles suka isa Garin Kuros Riba. ‘Yan kwallon sun je Garin ne domin daurin auren Ahmed Musa. Dan wasan na Najeriya ya aure Sahibar sa Juliet a Garin Kuros Ribas.

An daura Ahmed Musa da Sahibar sa Juliet a Garin su

‘Yan wasan Najeriya wajen zuwa bikin Ahmed Musa

A jiya 1 ga wata ne aka yi daurin auren gargajiyan ‘Dan wasan gaban nan na Super Eagles Ahmed Musa da kuma Sahibar sa Juliet Ejue a Garin Ogoja da ke Jihar asalin Kuros Ribas inda matar ta sa ta fito. Idan ba a manta ba Mahaifiyar sa dai ‘Yar Jihar Edo ce.

KU KARANTA: Shugaba Buhari na samun sauki - APC

An daura Ahmed Musa da Sahibar sa Juliet a Garin su

Wajen daurin gargajiyan Ahmed Musa da Juliet

Manyan ‘Yan wasan Super Eagles irin su Raheem Lawal sun isa har kauyen Mbube domin wannan babban taro. A baya dai an yi bikin auren wanda sai yanzu ne aka na asalin gargajiyar. Ahmed Musa dai ya rabu da Matar sa Jamila kafin yayi wannan aure.

A jiyan ne kuma babban Dan wasan Duniya Messi ya shiga daga ciki. Lionel Messi ya auri sahibar sa mai suna Antonella Rocuzzo wanda su ke tare su na yara.

An daura Ahmed Musa da Sahibar sa Juliet a Garin su

Ahmed Musa da Sahibar sa Juliet a wurin biki

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ronaldo na bibiyar Mawakin Najeriya Davido a shafin Instagram

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel