Rashin lafiyar shugaba Buhari ya hana wasu Ambasadojin kasashen waje fara aiki a Najeriya

Rashin lafiyar shugaba Buhari ya hana wasu Ambasadojin kasashen waje fara aiki a Najeriya

-Rashin lafiya Shugaba Buhari ya kawo jinkiri wajen fara aikin wasu ambasadoji a Najeriya

-Kasashen da abin ya shafa sun hada Egypt, Mexico, Greece, Vietnam da sauran su

-Wasu daga cikin ambasadojin sun iso Najeriya a kala wata biyu da suka wuce

Rashin lafiyar shugaba Muhammadu Buhari ya hana ambasadojin a kala guda goma daga kasahen duniya fara aikin su a kasar Najeriya.

Jaridar punch ta bada rahoton cewa ambasadojin sun iso Najeriya tun watani biyu da suka wuce amma basu samu daman ganawa da shugaba Buharin ba domin ya sa musu hannu a takardar kama aikin nasu.

Rashin lafiyar shugaba Buhari ya hana wasu Ambasadojin kasashen waje fara aiki a Najeriya

Rashin lafiyar shugaba Buhari ya hana wasu Ambasadojin kasashen waje fara aiki a Najeriya

Kamar yadda jaridar ta bada rahoto, ambasadojin sun hada da na kasar Bangladash, Egypt, Vietnam, Greece, Jam’uriar Benin, Mexico, Togo da kuma kasar Thailand. Rahotan yace wasikun nasu an aike su zuwa ga shugaba Buhari shiyasa Shugaba mai rikon kwarya Osinbanjo bai sa hannu akan sub a.

Wannan wasikar dai itace shaida da ke nuna cewa mai dauke da ita yana wakiltar kasar sa ne, kuma a al’ada shugaban kasa na sa hannu a takardan ne a huduwan san a farko da ambasodojin.

Wani babban jami’in daga fadar gwamnati wanda ya nemi a sakayi sunnan say a tabbatar da cewa ambasadojin kasashen ta abin ya shafa baza su iya aiwatar da aikin su yadda ya dace ba a yanzu har sai an tabbatar dasu din.

Amma ministan harkokin kasashen waje, Mista Godfrey Onyeama, yace ambasadojin su fara ayyukan su. Ya fada hakan ne a sakon karta kwana da ya aike daren jiya.

Babban sakatare da ma’aikatan harkokin kasashen waje, Ambasada Olusola Enikanolaiye yace mutenen da aka aiko a matsayin ambasadojin zasu fara aikin su da zaran an kammala aiwatar da abububwan da doka ta tsara.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel