Soja ga yaki ga boko: Wani Sojan sama yayi zarra a Jami’a

Soja ga yaki ga boko: Wani Sojan sama yayi zarra a Jami’a

– Wani Sojan sama na Najeriya ya ciri tuta wajen karatun sa na Digiri

– Babban Jami’i Enem Theophilus ya doke sauran Daliban Jami’ar

– Sojan ya kammala karatun Digirin sa na PhD yanzu haka

Wani Soja ya gama da maki 4.67 cikin 5.00 a karatun Digiri. Sojan ya kammala Digirin sa na uku kenan watau ya zama Dakta. Shugaban Hafsun Sojin yana kokari wajen ganin Sojoji sun tashi tsaye.

Soja ga yaki ga boko: Wani Sojan sama yayi zarra a Jami’a

Ga wuta ga littafi: Soja yayi zarra a Jami’ar Babcock

Wani Sojan saman Najeriya mai suna Enem Theophilus Aniemeka ya ciri tuta inda ya kammala Digiri na uku a Jami’ar Babcock ya kuma kare da maki 4.67 cikin 5.00. Yanzu haka dai wannan Babban Soja ya zama Dakta.

KU KARANTA: Rudunar Sojoji sun gano wasu bam-bamai

Soja ga yaki ga boko: Wani Sojan sama yayi zarra a Jami’a

Wani Sojan sama yayi zarra a Jami’ar Babcock

Enem Theophilus Aniemeka ya fara Digirin sa na Dakta ne a fannin sada bayanai ta na’urorin zamani a shekarar 2012. Sojan yayi wani nazari ne a wannan bangare wanda zai taimaka wajen kawo sauki a harkar kimiyyar komfuta na kasar.

Hakan dai ya nuna cewa ba kan bindiga kadai Sojin Najeriya su ka sani ba. Shugaban Hafsun Sojin saman kasar Air Marshall Abubakar Saddique yana kokari wajen ganin Sojoji sun kara sanin aiki.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Duniyar shakatawa: Ronaldo ya lalalubo Davido a yanar gizo

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel