Har yanzu ba a rasa na kwarai: Abin da wata Ma’aikaciyar Gwamnati tayi ya bada mamaki

Har yanzu ba a rasa na kwarai: Abin da wata Ma’aikaciyar Gwamnati tayi ya bada mamaki

– An yi kuskuren turawa wata Ma’aikaciya sama da Miliyan guda

– Da yake ta san ba na ta bane tuni ta maida wannan kudi inda ya dace

– Ko ashe dama akwai masu gaskiya irin wannan mata?

Albashin wannan Ma’aikaciya da ke Jihar Kogi bai wuce N30, 000 ba. Amma da wannan mata ta ga kusan Miliyan 2 a asusun ta sai ta maidawa Gwamnati. Bugu da kari dai Ma’aikatan Jihar na bin wani dogon bashi a halin yanzu.

Har yanzu ba a rasa na kwarai: Abin da wata Ma’aikaciyar Gwamnati tayi ya bada mamaki

Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello

Wata Ma’aikaciyar Gwamnati a Jihar Kogi ta maida sama Miliyan 1.78 da aka tura mata a asusun bankin ta. Albashin wannan Ma’aikaciya dai bai wuce N35, 000 a wata ba amma duk da haka ba tayi wata-wata ba ta maida kudin.

KU KARANTA: Zan maida Kogi tamkar Legas - Gwamna Bello

Wannan Ma’aikaciya mai suna Husseina Muhammad akanta ce don haka bayan ta sanar da iyalin ta sai ta garzaya wajen wani babban Jami’in Gwamnati domin maida wannan kudi. Ita dai rokon ta a biya Mijin ta albashin sa da yake bi na sama da shekara guda.

Ranar Juma’a kun ji cewa jim kadan bayan bayan CBN ya saki wasu makudan Daloli na Miliyoyi sai da Naira ta doke Dalar Amurka. Kwanan nan dai babban bankin na CBN ya saki wasu Dala Miliyan 195 a kasuwa domin a samu sa’ida.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Duba ka ga yadda ake maganin cutar taifod

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel