Biyafara: Jam’iyyar PDP tayi kaca-kaca da Nnamdi Kanu

Biyafara: Jam’iyyar PDP tayi kaca-kaca da Nnamdi Kanu

– Shugaban bangaren PDP Makarfi ya soki Nnamdi Kanu

– Ahmed Makarfi yace yunkurin na sa na kawowa kasa cikas

– Ya kara da cewa sam abin da Kanu yake yi ba daidai bane

Jam’iyyar adawa tayi tir da tafiyar Nnamdi Kanu. Bangaren Ahmed Makarfi dai na Jam’iyyar yayi Allah-wadai. Makarfi ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi.

Biyafara: Jam’iyyar PDP tayi kaca-kaca da Nnamdi Kanu

Kanu na jefa Najeriya cikin matsala-Inji PDP

Shugaban wani bangaren Jam’iyyar PDP Ahmed Muhammad Makarfi ya soki Nnamdi Kanu da fafutukar da yake yi wajen neman kasar Biyafara. Makarfi yace sam abin da yake yi ba daidai bane a wata hira da yayi da gidan talabijin Channels.

KU KARANTA: Ibrahim Magu ya fadi abin da ya dace ayi a Sambisa

Biyafara: Jam’iyyar PDP tayi kaca-kaca da Nnamdi Kanu

Makarfi yayi kaca-kaca da Nnamdi Kanu

Ahmed Makarfi yace har gara ‘Yan Arewar nan da su kayi kira Inyamurai su bar kasar da irin yunkurin da Nnamdi Kanu yake yi. Makarfi yace hanyar da Nnamdi Kanu ke bi na kawowa tattalin arzikin kasar cikas.

Kwanan nan mu ka samu wani sako da ake barazana ga ‘Yan Arewa mazauna Kudancin Najeriya. A sakon dai an nemi ‘Yan Arewa su tattara ina su-ina su su bar kasar kafin farkon wannan wata na Yuli.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Dubi wani Bidiyo game da Yakin Biyafara

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel