Daliban jami'a guda biyu sun mutu a yayin da suke daukan hoto a kwale-kwale

Daliban jami'a guda biyu sun mutu a yayin da suke daukan hoto a kwale-kwale

-Kwale-kwale ta kife da daliban jami’a a yayin da suke daukan hotuna

-Tsautsayi ya afka ma daliban jami’an tarayya da ke Akure su biyu.

-Muna bakin ciki da juyayi a bisa rashin yan uwan mu

Wasu dalibai guda biya yan jami’iar tarayya da ke garin Akure na jihar Ondo sun rasa rayunkan su bayan kwale-kwalen da suke ciki ta kife dasu a cikin rafin. Al’amarin ya faru ne a lokacin da daliban ke kokarin daukan hoton kansu da wayar sallula.

Daliban dai wadanda suke shekarar su ta uku a jami’ar sune Olabayi Emmanuel da kuma Olukun Babatunde.

Daliban jami'a guda biyu sun mutu a yayin da suke daukan hoto a kwale-kwale

Daliban jami'a guda biyu sun mutu a yayin da suke daukan hoto a kwale-kwale

Shugaban dalibai na jami’an mai suna Comrade Olaseinde Adeyinka ya tabbatar rasuwar daliban a wata sanarwa kamar haka, “Muna bakin ciki da juyayin sanar da rashin yan uwan mu da mukayi, Olabiyi Emmanuel daga sashin nazarin harkan noma da muhalli, da kuma Olokun Babatunde Alex daga sashen kimiyyar gudanar da ayyuka.

KU KARANTA: Boko Haram ta caccaki Kukasheka

“Labarin da muka samu yace daliban sunje dakin koyan aiki ne na fanin kamun kifi dake bayan dakin taro na Obakekere.

“Bayan sun sun gama aikin su, su hudu suka shiga cikin kwale-kwalen da aka ajiye a gefen rafin domin su dauki hotuna, a lokacin da suke daukan hotunan ne kwale-kwalen ta kife dasu, mutum biyu daga cikinsu sun iya ninkaya suka fitar da kansu, amma sauran biyun basu iya ba wanda shine sandiyar mutuwam nasu.

“Muna amfani da wannan daman domin muyi masu bankwana na karshe.”

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu, Inji Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu, Inji Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC
NAIJ.com
Mailfire view pixel