Babu inda za mu je; Mu na nan a Arewa Inji Inyamurai

Babu inda za mu je; Mu na nan a Arewa Inji Inyamurai

– Shugabannin Inyamurai sun ce ba za su bar Arewa ba

– Cif Eze Cletus Ilomuanya ya fadi wannan magana

– Mai martaba Eze shi ne Shugaban Sarakunan Kasar Ibo

Shugaban Sarakunan Kasar Ibo yace su na nan a Arewa. Sarkin ya bayyana abin da ya sa ba za su bar Yankin ba. Wasu na ta kira a raba a kasar a halin yanzu.

Babu inda za mu je; Mu na nan a Arewa Inji Inyamurai

Ba za fa mu bar Arewa ba Inji Shugabannin Inyamurai

Shugaban Sarakunan Kasar Ibo Cif Eze Cletus Ilomuanya yace Mutanen su ba za su bar Yankin Arewacin kasar nan ba duk da barazanar da ke yawo. Sarkin yace dokar kasa ta ba kowa damar zama inda ya ga dama.

KU KARANTA: Gwamnan Borno yayi alkawari ga Inyamurai

Babu inda za mu je; Mu na nan a Arewa Inji Inyamurai

Wasu na kira a raba kasar Najeriya

Sarkin yayi wannan magana ne a Garin Owerri na Jihar Imo lokacin da ya gana da wata Kungiya ta Matasan Inyamurai. Cif Eze Ilomuanya ya kuma gargadi Inyamuran da ke Arewa su zauna lafiya tare da gudun fitina.

Shugaban bangaren Jam’iyyar PDP Ahmed Muhammad Makarfi ya soki Nnamdi Kanu da fafutukar da yake yi wajen neman kasar Biyafara. Makarfi yace sam abin da yake yi ba daidai bane a wata hira da yayi da gidan talabijin Channels.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ojukwu da Yakin Biyafara [Bidiyo]

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel