Jami'iyar APC zata kafa kwamiti domin kawo sauyi a tsarin Najeriya

Jami'iyar APC zata kafa kwamiti domin kawo sauyi a tsarin Najeriya

-Zamu kafa kwamiti da zai kawo sauyi a tsarin Najeriya da kowa zai amince dashi

-Baza mu bari wata kungiya ta hana gudanar da zaben gwamna a jihar Anambra ba

-A shirye muke da mu saurari koke-koken mutane kuma bazamu tauye wa kowa hakinsa ba.

Bayan kiraye-kiraye daga kungiyoyi da mutane masu zaman kansu musamman yan kudancin Najeriya domin yin sauye-sauye a cikin yadda ake kasafta arzikin Najeriya, Jami’iya mai mulki a yanzu ta APC ta ce zata kafa kwamiti da zai duba al’amarin.

Jami’iyar ta cin ma wannan matsayan ne a wani taro da ya samu hallartan shugabanin jami’iyar da kuma gwamnonin APC wanda aka yi a ranar Alhamis a masaukin gwamnan jihar Imo da ke Asokoro a Abuja.

Wata majiya da ta samu hallartan taron ta ce kwamitin zai hada da gwamnoni, shugabanin jami’iyar da kuma yan majilissan kasa na jami’iyar.

Jami'iyar APC zata kafa kwamiti domin kawo sauyi a tsarin Najeriya

Jami'iyar APC zata kafa kwamiti domin kawo sauyi a tsarin Najeriya

Daya daga cikin gwamnonin yace ana sa ran kwamitin zai samo hanyoyin da zasu samar da dawamamiyar zaman lafiya da hadin ka a Najeriya.

“Mun tattauna zaben gwamna mai zuwa da za’a yi a jihar Anambra, musamman barazanar tada zaune tsaye da yan kungiyar IPOB ke yi, shugabani da gwamnonin kudu maso gabashin Najeriya da suka hallarci taron sun tabbatar mana cewa umarnin kungiyar IPOB na hana mutanen fitowa kada kuri’ar su bazai yi wani tasiri ba” Inji gwamnan.

Bayan kammala taron shugaban jami’iyar APC na kasa Chif John Ogidie-Oyegun shaida ma manema labarai cewa sun tattauna muhimman abubuwa a taron cikin su harda matsalolin da ke tasowa daga bangarori daban-daban na kasan nan.

“Niyyar mu shine mu karfafa jami’iyar mu, duk mun amince da cewa irin maganganun batanci da raba kan jama’a dake fitowa daga bangarorin kasan nan ba zai haifar mana da mai ido ba.

“Saboda haka zamu dauki kwararan matakai domin tabbatar da hadin kan kasan nan wanda bazan iya fada a nan ba, zamu tabbatar ko wane dan kasa an bashi hakin sa kuma an saurare koke-koken jama’a domin samun mafita.” Inji John Oyegun

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel