Kogi zata kama jihar Legas nan gaba kadan – Inji gwamnan Kogi

Kogi zata kama jihar Legas nan gaba kadan – Inji gwamnan Kogi

- Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce zai maida jihar kamar Legas

- Gwamna Bello ya ce yana aikatar da ayyuka daban daban don tabbatar da hanzarta ci gaban jihar

- Gwamnan ya musanta zargin cewa yana da hannu ga al’amarin sanata Dino Melaye wanda ake kokarin a masa kiranye daga majalisar dattijai

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce gwamnatinsa tana aiki gadan gadan don tabbatar da hanzarta ci gaban jihar.

Gwamnan ya ce kokarin da gwamanatin jihar ke yi yanzu haka babu shaka nan gaba kadan jihar zata kama jihar Legas a fanin ci gaba.

Gwamna Bello ya sanar da haka ne yayin da yake magana da manema labarai a Abuja a ranar Juma'a, 30 ga watan Yuni.

Kogi zata kama jihar Legas nan gaba kadan – Inji gwamnan Kogi

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello

Bello ya ce Jihar Kogi na ci gaba, yanzu jihar ta farfado daga barci kuma tana yunkurin cimma jihohin da suka sha gaban ta.

“A matsayin wakilin na matasa, ina samar da jagoranci na gari a jihar Kogi”. A cewar Bello.

Gwamnan ya kar yata jita jitar cewa akwai rikicin siyasa a jihar, ya ce ana zaman lafiya a jihar.

KU KARANTA: Gwamna Dankwambo na jihar Gombe ya hana ‘yan siyasa r jihar lika fastoti 'barkatai'

Gwamnan ya kuma bayyana cewa ba shida hannu ga al’amarin sanata Dino Melaye dan majalisa mai wakiltar mazabar Kogi ta yamma wanda ake kokarin a masa kiranye daga majalisar dattijai.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel