Yan sandan Najeriya sun samu gagarumar nasara kan wani shahararren barawon motoci

Yan sandan Najeriya sun samu gagarumar nasara kan wani shahararren barawon motoci

Rundunar yansandan Najeriya reshen jihar Enugu dake a kudancin kasar tace ta kama wani mutum wanda ya kware wajen satar motocin mutane da ya addabi jihar.

Shidai wannan barayon an ruwaito cewa yana anfani ne da makullin nan na musamman dake bude ko wace irin mota watau 'Master Key' a turance.

Yan sandan Najeriya sun samu gagarumar nasara kan wani shahararren barawon motoci

Yan sandan Najeriya sun samu gagarumar nasara kan wani shahararren barawon motoci

NAIJ.com ta samu labarin cewa an dai kama barawon ne a dai-dai lokacin da yake kokarin satar wata mota a katafaren kamfanin nan na saide-saide na Shoprite dake a garin na Enugu.

Mai magana da yawun yan sandan har ila yau ya bayyana cewa an samu makudan kudade a kugun barawon tare kuma da sauran makullan da ake kyautata zaton na sata ne.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel