Likitocin Buhari sun ce ba zai iya tabuka wani abu ba – Fani Kayode ya yi ikirari

Likitocin Buhari sun ce ba zai iya tabuka wani abu ba – Fani Kayode ya yi ikirari

- Matsayin lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari na kewaye da jayayya da dama

- Shugaban kasar ya yi tafiyar jinya karo na biyu a birnin Landan kan wani rashin lafiya wanda shi da mataimakansa suka ki bayyana wa ‘yan Najeriya ainahin cutar dake damun sa

- Femi Fani-Kayode ya yi ikirarin cewa likitocin Buhari sunce ba zai iya kuma aiki ba wanda shine dalilin da ya sa bai dawo kasar ba

Tsohon ministan dake kula da sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya bayyana shugaban jam’iyyar APC, John Odigie-Oyegun a matsayin makaryaci.

Fani-Kayode na maida martani ne ga wani sanarwa da Oyegun ya yi a kan lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa shugaban APC ya bayyana wa manema labarai a ranar 30 ga watan Yuni, cewa shugaban kasar na samun sauki sosai sabanin zargin cewa bai san inda kansa yake ba.

Da yake maida martani, Fani-Kayode ya bukaci Oyegun da ya daina karya.

A cewar sa duk kokari da ake yin a dawo da shugaban kasar ya gaza kamar yadda likitocin sa suka bayyana cewa ba zai iya aiki ba.

KU KARANTA KUMA: YANZU YANZU: Sakatariyar tarayya Abuja ta kama da wutaYANZU YANZU: Sakatariyar tarayya Abuja ta kama da wuta

Da yaje shafin san a twitter, Fani-Kayode ya rubuta: “Duk kokari da ake na dawowa da Buhari Najeriya daga Ladan ya kuma shan ruwa kamar yadda likitocin sa suka bayyana gazawarsa gun aiki.

Shugaban kasa Buhari ya bar kasar a ranar 7 ga watan Mayu domin ganin likita karo na biyu, don wani rashin lafiya da ba’a bayyana wa ‘yan Najeriya ba.

Sakamakon rashin sa a kasar, Gwamna Ayodele Fayose ya yi ikirarin cewa Buhari na nan bai san inda kansa yake ba tun ranar 6 ga watan Yuni a wani asibitin Landan.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel