Zaben 2019: Wata kungiya ta nuna goyon bayanta ga Lamido a matsayin shugaban kasa

Zaben 2019: Wata kungiya ta nuna goyon bayanta ga Lamido a matsayin shugaban kasa

- Kungiyar North East Democratic Enlightenment Initiative (NDEI) ta nuna goyon bayanta ga tsohon gwamnan jihar Kaduna, Sule Lamido da ya tsaya takarar shugabancin kasar a shekarar 2019

- Shugaban kungiyar ya yi kira ga ‘yan Najeriya da suyi gangami a kan tsohon gwamnan wanda yace shine mafita ga kalubalen da kasar ke ciki na koma bayan tattalin arziki idan har suka zabe shi

- Ya bayyana Lamido a matsayin dan siyasa da ya kware, gogagge, sannan kuma dan Najeriya da baida nuna bambanci

Wata kungiyar Arewa maso gabas mai suna North East Democratic Enlightenment Initiative (NDEI) ta nuna goyon bayanta ga tsohon gwamnan jihar Kaduna, Sule Lamido da ya tsaya takarar shugabancin kasar a shekarar 2019.

Shugaban kungiyar, Aliyu Garkuwa, yayinda yake magana a Bauchi, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da suyi gangami a kan tsohon gwamnan wanda yace shine mafita ga kalubalen da kasar ke ciki na koma bayan tattalin arziki idan har suka zabe shi.

KU KARANTA KUMA: YANZU YANZU: Sakatariyar tarayya Abuja ta kama da wuta

Ya bayyana Lamido a matsayin dan siyasa da ya kware, gogagge, sannan kuma dan Najeriya da baida nuna bambanci.

Shugaban kungiyar ya tuna rawar ganin da Lamido ya taka a lokacin da yake a matsayin shugaban matasan jam’iyyar Peoples Redemption Party (PRP) a tsohuwar jihar Kano wanda ya kai ga nasarar jam’iyyar a zaben 1979 a jihohin Kano da Kaduna.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyo na NAIJ.com:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel