An maka wani matashi kotu kan shiga tarzoman neman sako El Zakzaky

An maka wani matashi kotu kan shiga tarzoman neman sako El Zakzaky

- An gurfanar da wani matashi a gaban kotu bisa zargin cewa ya shiga tarzoman neman a saki shugaban kungiyar shi'a

- Kotu ta ba da belin sa kan kudi naira dubu dari

- Zakzaky da matarsa na tsare kusan tsawon shekaru biyu kenan

Rahotanni sun kawo cewa an kama wani magidanci da aka ambata da suna Mubarak Sa’idu sannan aka gurfanar da shi a gaban wata kotu dake babban birnin tarayya Abuja kan zargin cewa ya shiga hatsaniyan neman a sako shugaban kungiyar musulmai mabiya shi’a, Malam Ibrahim El-Zakzaky.

An kama matashin ne wanda ya kasance dan asalin jihar Kano a lokacin da suke gudanar da zanga-zangar a masallacin babban birnin tarayya Abuja ba bisa ka’ida wato basu nemi izinin yin hakan ba, wanda hakan ya keta doka.

KU KARANTA KUMA: Kamfanonina za su iya ceto Najeriya daga dogaro da mai - Dangote

An maka wani matashi kotu kan shiga tarzoman neman sako El Zakzaky

An maka wani matashi kotu kan shiga tarzoman neman sako El Zakzaky

Zuwa yanzu dai matashin ya karyata zargin sai dai alkalin kotun, mai shari’a Umar Kagarko ya ba da belin sa kan kudi naira dubu dari (N100,000).

Idan ba’a manta ba, a ranar 2 ga watan Disambar bara ne NAIJ.com ta ruwaito wata babbar kotu dake zamanta a Abuja ta bada umarnin a saki shugaban kungiyar shi’a Ibrahim Zakzaky.

Shugaban kungiyar na Shi’a tare da matarsa na tsare kusan shekaru biyu kenan tun bayan tarzoma da akayi tsakanin mabiya addinin da rundunar sojin Najeriya a shekarar 2015.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Labarin wani tsohon sojin Biyafara:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel