Kamfanonina za su iya ceto Najeriya daga dogaro da mai - Dangote

Kamfanonina za su iya ceto Najeriya daga dogaro da mai - Dangote

- Dangote ya ce kamfanoninsa za su taimaka gurin ceto Najeriya daga dogaro da mai

- Ya ce hakan zai yiwu ne saboda gwamnati mai ci a yanzu ta mayar da hankali gurin ganin kasar ta daina dogaro da mai kamar yadda ta ke yi a baya

Mai kudin Afrika , Alhaji Aliko Dangote ya sha alwashin cewa kamfanoninsa za su iya taka rawar gani sosai wajen ceto Najeriya daga al'adar dogaro da mai wajen samun kudaden shiga.

Dangote ya ce tun a shekarar 1978 aka fara maganan rage dogaro da mai amma duk gwamnatoci da suka shude sun gaza yin komai a kan haka amma a cewarsa, gwamnati da ke ci yanzu ta mayar da hankali matuka wajen ganin kasar nan ta daina dogaro da mai inda ya kara da cewa lokaci ya yi da za a fara sa ido kan attajiran kasar nan kan rawar da suke takawa wajen samar da ayyukan yi ga matasa.

KU KARANTA KUMA: Ra’ayin Dangote game da wa’adin da aka baiwa Inyamurai a Arewa

Kamfanonina za su iya ceto Najeriya daga dogaro da mai - Dangote

Kamfanonina za su iya ceto Najeriya daga dogaro da mai cewar Dangote

Idan zaku tuna a baya NAIJ.com ta rahoto cewa Dangote ya yi ikirarin samar da ayyukan yi ga daukacin matasan Najeriya da zaran aka kammala aikin matatar man fetur din shi.

Ya fadi hakan ne a lokacin da ya ke tofa albarkacin bakin shi a kan wa’adin da wasu matasan Arewa suka diba ma ‘yan kabilar Igbo, inda ya bayyana hakan a matsayin rashin aikin yi.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel