Inyamurai sun nemi ‘Yan Arewa su bar masu kasa kafin gobe

Inyamurai sun nemi ‘Yan Arewa su bar masu kasa kafin gobe

– Kwanan nan mu ka samu wani sako da ke barazana ga Inyamurai

– An yi kira ga ‘Yan Arewa da ke Kudu su garzaya su bar Yankin

– Ana dai ta irin wadannan yunkuri a halin yanzu a kasar

An nemi ‘Yan Arewa mazauna Yankin su bar Kudancin kasar zuwa gobe. A sakon da ya fito tun kwanaki an ba ‘Yan Arewa wa’adi zuwa wannan wata. Haka dai kwanaki wasu ‘Yan Arewa su ka kira ‘Yan kudu su bar masu kasa.

Inyamurai sun nemi ‘Yan Arewa su bar masu kasa kafin gobe

An yi wa ‘Yan Arewa da ke Kudu barazana

Mun samu wani sako da ake barazana da ‘Yan Arewa mazauna Kudancin Najeriya. A sakon dai da ba a san daga inda ya fito ba an nemi ‘Yan Arewa su tattara ina su-ina su su bar kasar kafin gobe wanda ita ce Ranar farko na watan Yuli.

KU KARANTA: Turawa sun yi Hawan Sallah a Arewa

Inyamurai sun nemi ‘Yan Arewa su bar masu kasa kafin gobe

Inyamurai sun yi wa ‘Yan Arewa barazana

A sakon da aka fitar an yi kira ga Mazauna Yankin da kakkasusar murya su bar Kasar Kudu ko kuma su ga abin da zai faru da su. A sakon mai maganar yace yana da makaman da zai yaki Hukuma babu kakkautawa.

Mun samu labari cewa kwanaki 27 ga Watan nan ne Gwamna Nyesom C Wike na Jihar Ribas ya kai ziyara har fadar Sultan watau Sarkin Musulmi Abubakar Sa’ad III tare da tawagar sa ta Sarakunan gargajiya a Jihar Sokoto inda yace ba ya goyon bayan a raba Najeriya.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyo game da Yakin Biyafara

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel