APC ta ba da bayani a kan lafiyar Buhari, ta yi tsokaci a kan lokacin dawowar shugaban kasar

APC ta ba da bayani a kan lafiyar Buhari, ta yi tsokaci a kan lokacin dawowar shugaban kasar

- Shugaban APC ta kasa, John Odigie-Oyegun ya ce shugaba Buhari zai dawo gida Najeriya bayan likitansa ya tabbatar da ya samu lafiyan yin haka

- Oyegun ya ce shugaban kasar na samun sauki cikin sauri

- Shugaban Jam’iyyar ta bayyana cewa shugaban jam’iyyar na da kyakkyawan yakini a kan shugaba Buhari

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari na samun sauki cikin sauri daga rashin lafiyarsa sabanin zargin cewa bai san inda kansa ya ke ba.

Shugaban jam’iyyar, Cif John Odigie-Oyegun, ne ya ba da tabbacin a Abuja a ranar Juma’a, 30 ga watan Yuni, yayinda yake zantawa da manema labarai a karshen wata ganawa tsakaninsa da kwamitin aiki na jam’iyyar da kuma gwamnonin jam’iyyar.

KU KARANTA KUMA: Wani dan Najeriya mai basira ya kera motoci a jihar Kebbi

Oyegun ya kuma bayyana cewa Buhari zai dawo kasar ne bayan likitocinsa na waje sun amince da ya yi hakan, kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ta ruwaito.

Idan zaku tuna Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose ya bayyana cewa shugaban kasa Buhari bai san inda yake ba a wani asibitin Landan inda yake samun kulawar likita.

Amma shugaban jam’iyyar bai maida martani ga furucin gwamnan ba, cewa zai yi hakan a lokacin da ya kamata.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel