Kungiyar Inyamurai ta soki tsohon Shugaban kasa Babangida

Kungiyar Inyamurai ta soki tsohon Shugaban kasa Babangida

– Tsohon Shugaba I.B.B ya ga uwar-bari game da kalaman sa

– Janar Ibrahim Babangida yayi kira ayi wa Najeriya garambawul

– Tsohon Gwamna Adams Oshimole ya caccaki tsohon Shugaban

Kalaman Janar Babangida sun jawo ce-ce-ku-ce a Najeriya. Tsohon Shugaban kasar dai ya nemi a sauyawa Najeriya tsari. IBB ya kuma yi kira da a guji tada hankali ko jawo fitina.

Kungiyar Inyamurai ta soki tsohon Shugaban kasa Babangida

Tsohon Shugaban kasa IBB ya na ganin uwar-bari

Sakataren Kungiyar ECA ta Majalisar Inyamuran Najeriya yayi watsa-watsa da kiran da Tsohon Shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida yake yi na a ayi wa Najeriya garambawul. A cewar ta sai yanzu ne tsohon Shugaban kasar ya baro rakiyar akidar sa ta da.

KU KARANTA: Yau Dan wasa Lionel Messi ya zama Ango

Kungiyar Inyamurai ta soki tsohon Shugaban kasa Babangida

An dura kan IBB bayan yayi kira ayi wa Najeriya garambawul

Kungiyar ta ECA tace ba ta yarda a yi wani garambawul da za a cigaba da zama da Jihohi 36 ba. Evang Eliot Uko ya bayyana haka. A da baya dai kungiyar ta zargi tsohon shugaban da kin yi wa kasar garambawul din da ake magana.

Shi kuma Tsohon Gwamnan Edo Oshimole yana cewa Babangida ya kashe kasar nan. Adams Oshimole ya caccaki tsohon Shugaba Janar Babangida. Haka shi ma dai Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya tofa albarkacin bakin sa game da batun.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel