Hakar CBN ya ci ma ruwa: Naira ta doke Dala a kasuwar canji

Hakar CBN ya ci ma ruwa: Naira ta doke Dala a kasuwar canji

– Darajar Naira tayi sama jiya a kasuwar canji

– Yanzu Naira ta buge Dalar Amurka a kasuwar canji

– Hakan na zuwa bayan CBN ya saki wasu Dalolin Miliyoyi

Ana ganin amfanin tsarin babban bankin CBN . Yanzu Dalar Amurka ta dan yi sauki a kasuwa. Dalar Amurka ta rage tsada da N3 a hannun ‘yan canji.

Hakar CBN ya ci ma ruwa: Naira ta doke Dala a kasuwar canji

Madalla: Naira ta doke Dala a kasuwar canji

Jim kadan bayan bayan CBN ya saki wasu makudan Daloli na Miliyoyi sai da Naira ta doke Dalar Amurka. Kwanan nan dai babban bankin na CBN ya saki wasu Dala Miliyan 195 a kasuwa domin a samu sa’ida.

KU KARANTA: Aure ya karbi Sarauniyar kyau ta Duniya

A makon jiya dai an saida Dalar ne a kusan N370 wanda yanzu haka an samu ragi na har N3. Dalar yanzu da mu ke magana tana kan N367 ne a hannun ‘Yan kasuwa. CBN na cigaba da sakin Daloli domin farashi yayi sauki.

Kwanaki wani babban Jami’in CBN ke cewa tattalin arzikin Najeriya zai zabura zuwa karshen shekarar nan. Sanannen abu ne dai cewa Najeriya na cikin matsin tattali kusan tun bayan hawan Shugaba Buhari wanda yanzu abubuwa sun kama hanyar mikewa.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel