Kotu ta aike da dattijiya yar shekara 64 kurkuku akan safarar kwaya

Kotu ta aike da dattijiya yar shekara 64 kurkuku akan safarar kwaya

- Kotu ta yanke ma mata yar shekara 64 hukuncin shekara 25 a gidan yari

- A yanke hukuncin ne ba don musguna ma mai laifin ba, sai dai don ya zama hanya gyara – inji Alkali Rabiu-Shagari

- Manyan mata a Legas sunyi yunkurin safaran hodar iblis zuwa kasar Saudiya.

Wata babban kotu da zama a garin Legas ta yanke wa Odeyemi Omolola yar shekara 64 hukunci shekara 25 a gidan yari. Hukuncin ya biyo bayan kama ta da akayi ne da hodar iblis wanda nauyin shi ya kai kilo gram 1.595 zuwa kasar Saudiya. Bincike ya nuna tana aiki tare da wata mata mai suna Mrs Funmilola Ogundipe wanda aka fi sani da Ariket.

Alkali Hadizat Rabiu-Shagari wanda ta zartar da hukuncin tace an same mai laifin ne da da laifuka har guda biyar.

Ita Ariket wanda sananiya ce a Legas an same ta da laifukan da suka hada da samo haramtaccen kwaya, taimaka wa wajen safaran kwayan da yi ma doka zagon kasa.

Kotu ta aike da dattijiya yar shekara 64 kurkuku akan safarar kwaya

Kotu ta aike da dattijiya yar shekara 64 kurkuku akan safarar kwaya

Laifufukan inji lauya mai shigar da kara, Mista Abu Ibrahim sun ci karo da sashi na 14(b), 11(b) da kuma sashi na 19 na Dokar Yaki da Fataucin miyagun kwayoyi na tarayyar Nigeria na shekara 2004.

Mutane biyun da ake tuhuma dai duk sun amsa laifinsu da aka gabatar dasu gaban kotu a watan mayun wannan shekaran amma daga baya daya daga cikin matan Mrs Omolara tayi yunkurin canza amsa laifin da tayi a baya wanda ya danganci kokarin safaran hodar iblis zuwa kasar Saudiya.

Alkali Rabiu-Shagari ta bada daman a sake karanta mata tuhumar da ake mata. Bayan an sake karanta mata, ta amsa laifin ta. Lauya mai shigar da kara ya bukaci kotu da ta tabbatar da laifin kuma abashi lokaci ya sake bibiyar bayanan karar.

Lauya mai kare masu laifi yayi kokarin jinkirta hukunci amma hakan bai yiwu ba.

A yayin da take yanke hukunci, Alkali Rabiu-Shagari tace “Na saurari bayanin lauyar da ke kare wanda ake tuhuma, hukuncin da na yanke ba wai don musguna ba mai lafin bane sai dai kawai don gyara kuma domin ya zama misali ga wanda ke niyan aikata irin wannan laifin, na yanke ma wanda aka samu da laifi hukuncin shekara 25 a gidan yari.”

Alkali Rabiu-Shagari kuma bada umurnin kotu ta kwace passpo da tkitin jirgin Egypt air domin ajiye wa a wajen hukuma.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel