Yawan Musulmai a birnin Sydney na ƙasar Australia ya haura 253,435

Yawan Musulmai a birnin Sydney na ƙasar Australia ya haura 253,435

- Musulman kasar Australia sun kara yawa a shekarun nan

- Yawan Musulmai sun karu daga 341,000 zuwa 604,000

Wani kidayan jama’a da aka yi a shekarar 2016 na kasar Australia ya nuna cewa sama da rabin Musulman kasar Australia na zama ne a babban birnin kasar, Sydney.

Jaridar Daily Trust ta rwuaito yawan Musulmai a Sydney ya karu da kashi 5.3 a shekarar 2016, inda suka kai 253,436, kimanin kashi 40 kenan na jimillan Musulman kasar daya kai 604,000.

KU KARANTA: Minista Audu Ogbeh ya cika alƙawari: Najeriya ta fitar da doya cikin sunduƙai zuwa ƙasarAmurka (HOTUNA)

Kidayar al’ummar kasar ta bayyana addinin Musulunci a matsayin addinin daya fi samun cigaba a kasar Australia fiye da addinin Buddha, hakan ya mayar da shi a mataki na 2 a bayan addinin Kirista.

Yawan Musulmai a birnin Sydney na ƙasar Australia ya haura 253,435

Musulmai

Hakazalika, yawan Musulmai ya karu daga 341,000 a shekarar 2006 zuwa 604,000 a shekarar 2016, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ka goyi bayan kafa sabuwar jam'iyya?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel