Dandalin Kannywood: Kun san sabuwar jaruma Maryam Yahaya ta cikin fim din Mansoor?

Dandalin Kannywood: Kun san sabuwar jaruma Maryam Yahaya ta cikin fim din Mansoor?

- Hakika sabuwar jaruma Maryam Yahaya jaruwar da ta jagoranci fim din Mansoor ta taka muhimmiyar rawa duk kuwa da cewa sabuwar fuska ce.

- Jarumar ta dai fito ta taka muhimmiyar rawa a cikin fim din na Mansoor wanda ake sa ran fitar sa a yau din nan 30 ga watan Yuni kuma ko shakka babu tayi wa sauran jaruman fim din na Hausa fintinkau.

Wannan ne ma yasa kamfanin shirya fina finan nan na FKD ya tsaya tsayin daka wajen ganin ya haska ta a babban fim din na su.

Maryam Yahaya dai yar asalin garin Kano ce, ta kuma nuna kwarewarta a farfajiyar, gwana ce ta gwanaye, wadda take yin kyau da zarar an dora mata kyamara. Wani karin armashi game da ita shi ne, yadda ba ta wasa da aikinta a matsayin jaruma.

Dandalin Kannywood: Kun san sabuwar jaruma Maryam Yahaya ta cikin fim din Mansoor?

Dandalin Kannywood: Kun san sabuwar jaruma Maryam Yahaya ta cikin fim din Mansoor?

NAIJ.com ta samu labarin cewa bajintar da ta nuna a fim din, MANSOOR, duk da cewa ba shi fim na farko da ta fara fitowa ba, amma an ga yadda tauraruwarta ta haska shi ne ya janyo mata farin jini da daukaka kafin ya fita.

Tallansa kawai jama’a suka gani, amma suka tabbatar da cewar Maryam Yahaya za ta yi abun kirki a masana’antar fim.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel