Tirka-Tirka: Wasu yan jihar Kogi sun kai hukumar INEC kara kotu saboda Sanata Dino Melaye

Tirka-Tirka: Wasu yan jihar Kogi sun kai hukumar INEC kara kotu saboda Sanata Dino Melaye

Wasu gungun yan jihar Kogi da suke da suna The Concerned Kogi Registered Voters (CKRV) a turance da suka kai su 18 sun maka hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau INEC kotu saboda shirin kiranyen da zata fari yi wa Sanata Dino Melaye daga jihar.

Gungun yan jihar dai sun kai karan ne da nufin samun amincewar kotun wajen hana hukumar zaben ta Independent National Electoral Commission (INEC) a turance shirin ta na yiwa Sanatan nasu kiranye daga majalisar dattawan Najeriya.

Tirka-Tirka: Wasu yan jihar Kogi sun kai hukumar INEC kara kotu saboda Sanata Dino Melaye

Tirka-Tirka: Wasu yan jihar Kogi sun kai hukumar INEC kara kotu saboda Sanata Dino Melaye

NAIJ.com ta samu labarin cewa matasan sun kalubalanci yawan mutanen da akace sun sa hannu a rijistar yin kiranyen inda suka ce wasun su da yawa ma sun mutu da dadewa.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa mutane a kalla 188,000 ne suka sa hannu a rijista kuma suka aikawa hukumar INEC da nufin yi wa dan majalisar dattijai Dino Melaye kiranye a kwankin baya.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel