Minista Audu Ogbeh ya cika alƙawari: Najeriya ta fitar da doya cikin sunduƙai zuwa ƙasarAmurka (HOTUNA)

Minista Audu Ogbeh ya cika alƙawari: Najeriya ta fitar da doya cikin sunduƙai zuwa ƙasarAmurka (HOTUNA)

- An gudanar da bikin fara tura Doyar Najeriya zuwa ƙasashen Turai

- Bikin fara tura doyar ta samu halartan ministan harkokin noma, Audu Ogbeh

A jiya Alhamis 29 ga watan Yuni ne aka gudanar da bikin fitar da doyar Najeriya zuwa kasashen Turai da Amurka, kamar yadda ministan harkokin noma Audu Ogbeh yayi alkawari a baya.

An gudanar da bikin aika doyar ne a sansanin ajiye sundukai na Lillypond dake Ijora, jihar Legas, duk a yayin taron, Minista Ogbeh ya zagaya inda ya duba rumbunan zamani na ajiye doyar.

KU KARANTA: Rikici tsakanin jikan Sardauna da jigon APC tayi fallatsa har fadar Sarkin Musulmi

NAIJ.com Yawancin Doyan an noma su ne a jihar Binuwe,wanda hakan ya sanya gwamnan jihar, wanda ya samu wakilcin mataimakin gwamnan jihar, yin godiya ga gwamnatin Najeriya, da minista Ogbeh.

Minista Audu Ogbeh ya cika alƙawari: Najeriya ta fitar da doya cikin sunduƙai zuwa ƙasarAmurka (HOTUNA)

Minista Audu Ogbeh tare da baki

Cikin manyan baki da suka halarci taron sun hada da wakilin shugaban hukumar kwastam, shugaban hukumar tashoshin jiragen ruwa, shugaban cibiyar noma, IITA da sauran baki daga ciki da wajen kasar nan.

Minista Audu Ogbeh ya cika alƙawari: Najeriya ta fitar da doya cikin sunduƙai zuwa ƙasarAmurka (HOTUNA)

Minista Audu Ogbeh tare da baki

A jawbainsa, Minista Ogbeh yace wannan ba sabon abu bane, a baya dama ana yi, amma lalacewa ne tasa aka yi watsi da shi. Ministan yace duk Duniya babu kasar data kai Najeriya noman doya, don haka ake sa ran Najeriya zata samu sama da dala biliyan 4 daga cinikin doyar.

Minista Audu Ogbeh ya cika alƙawari: Najeriya ta fitar da doya cikin sunduƙai zuwa ƙasarAmurka (HOTUNA)

Rumbunan adanan doyan

Ita ma a nata jawabin, Hadiza Bala Usman, shugaban hukumar tashoshin jiragen ruwa ta bayyana farin cikinta da wannan abu, inda tace tayi murna da Najeriya ta fara fitar da doya, kuma tayi alkawarin bada dukkanin goyon bayan data dace.

Minista Audu Ogbeh ya cika alƙawari: Najeriya ta fitar da doya cikin sunduƙai zuwa ƙasarAmurka (HOTUNA)

Doyan rufe cikin kwali

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Dakin da Ojukwu ya boye a yakin Biyafara

Source: Hausa.naija.ng

Related news
PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan
NAIJ.com
Mailfire view pixel