An yankewa mataimakin shugaban makarantar da ya yi wa dalibarsa fyade hukuncin daurin rai-da-rai

An yankewa mataimakin shugaban makarantar da ya yi wa dalibarsa fyade hukuncin daurin rai-da-rai

Babban kotun jihar Ekiti ta yanke ma wani mataimakin shugaban wata makaranta na ‘yan mata dake jihar hukuncin daurin rai-da-rai bayan an kama shi da laifin yi wa ‘yarinya kuma dalibarsa mai shekaru 12 fyade.

Kotun ta ce laifin ya sabawa sashe na 31(2) na dokar kare hakkin kananan yara na jahar Ekiti wacce aka kafa a shekarar 2012.

A lokacin da ya aikata laifin, a watan Mayun 2014, Mista Ajayi shi ne mataimakin makaranta mai kula da sashen karatu.

Bisa ga rahoto, Mutumin mai suna Mista Ajayi ya kira yarinyar zuwa ofishin sa, bayan nan sai ya rufe ofishin na sa sannan ya far ma yarinyar ta karfin tuwo. Anyi ta bugun kofar a lokacin da al’;amarin ke faruwa amma yayi burus ya ki bude kofar.

KU KARANTA KUMA: Aure ya karbi Agbani Darego-Danjuma

An yankewa mataimakin shugaban makarantar da ya yi wa dalibarsa fyade hukuncin daurin rai-da-rai

An yankewa mataimakin shugaban makarantar da ya yi wa dalibarsa fyade hukuncin daurin rai-da-rai

Ya gurfana a gaban kotu a watan Oktoban shekarar 2016, amma ya ki amsa laifin sa.

Alkalin kotun, Oluwatoyin Abodunde ta ce bangaren masu kara sun tabbatarwa kotu tare da hujjoji masu karfi cewa wanda ake kara ya aikata wannan laifi.

Alkalin ta ce duba da yadda laifukan fyade ke kara yawaita, ya zama wajibi a yanke irin wannan hukunci domin ya zama izina ga na baya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel