Jihar Anambra ta tsame kanta daga Biyafara

Jihar Anambra ta tsame kanta daga Biyafara

- Bamu tare da duk wani mai gwagwarmayar kirkirar kasar Biyafara - inji Anambra Peoples Assembly

- Nnamdi Kanu ya bar nasa iyalen a Ingila amma yana so ya hallaka mana namu a Najeriya inji Okorafor

- Mutanen jihar Anambra masu bin doka ne kuma zasu fita kada kuri’ar su a zaben gwamna mai zuwa a jihar.

Yan asalin jihar Anambra jiya sun bada sanarwar cewa basu tare da wasu yan kabilar ibo da ke kokarin kafa kasar Biyafara. Sun bada wannan sanarwan ne a karkashin wata hadadiyar kungiyarsu mai suna Anambra Peoples Assembly.

Kungiyar tace mutanen jihar Anambra zasu fito kwan su da kwarkwata domin jefa kur’ar su a zaben gwamna da za’ayi a jihar kwanan nan.

A wata sanarwa da jagoran kungiyan Mazi Nnamdi Okorafor ya rattafawa hannu, kungiyar tace mutanen jihar Anambra masu bin doka ne kuma baza su yarda wani mutum ko kungiya ta tunzura su ba.

Jihar Anambra ta tsame kanta daga Biafra

Jihar Anambra ta tsame kanta daga Biafra

“Zan tabbatar cewa babu dattawa a kasar ibo, idan mu ka bari wani dan karamin yaro da tunzura mu muka fada yaki saboda maganganun batanci da raba kan jama’a.

“Nnamdi kanu yana rudan kansa ne kawai, nan gaba masu daure masa gindi zasu janye jiki su kyale shi. Shi da mabiyansa zasu gane sunyi kuskure. Ba kowane mutumin ibo bane ke goyon bayan kungiyar IPOB, kuma kasancewar ka shugaban IPOB bayan nufin kai shugaban kabilar ibo ne.” Inji Okorafor.

Yace Nnamdi Kanu rudaden mutum ne kawai wanda ya bar iyalinsa a kasar Ingila amma yazo Najeriya yana so ya hallaka mana namu iyalan.

Ya kara da cewa “Mun yarda da cewa kowane dan kasa yana da yancin neman a biya masa bukatunsa, amma duk da hakan, muna amfani da wannan damar mu sanar da kowa mutanen jihar Anambra sun tsame kansu daga duk wani yunkuri na kirkirar kasar Biyafara.

Duk masu neman Biyafara su bar jihar Anambra su tafi jihar su domin cigaba da gwagwarmayan. Baza mu yarda wani ya raina mana hankali ba. Yan asalin jihar Anambra zasuyi rajistan zabe kuma zasu fita su kada kuri’ar su idan lokacin zaben gwamna na shekara 2017 yayi.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel