Baza mu amince da duk wani sauyi da gwamnatin Buhari zatayi ba - Samarin Ohanaeze

Baza mu amince da duk wani sauyi da gwamnatin Buhari zatayi ba - Samarin Ohanaeze

- Shugaban kasa daga kudu ne kawai zaiyi adalci wajen yin sauyi a tsarin Najeriya

- Wasu shugabanin kabilar ibo suna son su kama shugaban kungiyan mu saboda muna goyon bayan kirkiran kasar Biafra- Ohanaeze Youths

- Gwamnatin shugaba Buhari baza tayi ma kabikar ibo adalci ba

Kungiyoyi daban-daban daga bangaren kudancin kasar Najeriya suna ta neman izinin kafa tasu sabuwar kasar da suke kira da Biafra. Wannan dai ba sabon abu bane idan mukayi la’akari da cewa wannan yunkurin ya samo asali ne tun shekaru tun shekarar 1967 a lokacin da Odemegwu Ojukwu ya jagoranci yunkurin ballewar amma dai abin bai yiwu ba.

A halin yanzu kawunan kabilar ibon ya kasu kasha biyu ne, akwai wadanda suke so ayi ma kudin tsarin Najeriya gyara domin a kara ma kudu Kason kudi da gwamnatin tarayya ke bata sannan akwai wadanda kawai sun kasar su suke so a bari su kafa wata kasar Biafra.

KU KARANTA KUMA: Aure ya karbi Agbani Darego-Danjuma

Baza mu amince da duk wani sauyi da gwamnatin Buhari zatayi ba - Samarin Ohanaeze

Baza mu amince da duk wani sauyi da gwamnatin Buhari zatayi ba - Samarin Ohanaeze

Wata kungiya mai suna “Ohanaeze youths” sunce su bazu taba amincewa da wata gyara ko sauyi da gwamnatin Shugaba Buhari zata yi.

Kungiyar tace babu wani shugaba daga arewacin Najeriya da zaiyi ma kudu adalci, saboda haka zasu amince ayi gyaran ne idan Shugaba daga kudancin Najeriya ya dare karagar mulkin Najeriya.

Sakataren kungiyar, Mazi Oku Nnabuike yace idan Shugaba daga kudu zaiyi gyaran, toh ko shakka babu zaiyi wa kowa adalci a Najeriya.

Kungiyar har illa yau tana zargin cewa akwai wasu shugabanin kabilar ibon da ke son cafke shugaban kungiyan mai suna Maxi Okechukwu Isiguzoro akan goyon bayan samar da kasar Biafra.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel