An tura samfurin maganin kwaya cutar HIV a yankin Afrika

An tura samfurin maganin kwaya cutar HIV a yankin Afrika

- An kaddamar da wani sabon maganin mai warkar da kwayar cutar HIV

- Za a sayar da sabon maganin kwayar cutar HIV farashi mai rahusa ga mabukata

- A nan gaba kadan maganin zai isa kasashen Najeriya da Uganda

An kaddamar da wani sabon samfurin maganin kwaya cutar HIV a yankin Afrika, Za a sayar da wannan magani akan farashi mai rahusa ga mabukata.

Sabon samfurin maganin na DTG da aka fara kaddamarwa a kasar Kenya, zai bai wa talakawan da ke dauke da cutar damar sayan sa kan farashi mai rahusa.

KU KARANTA: Kotu ta yassare ma iyaye daman kashe ýaýansu jarirai a wata ƙasa, Karanta

A Wannan shekara ta 2017 ana tsamani maganin zai isa kasashen Najeriya da Uganda.

An tura samfurin maganin kwaya cutar HIV a yankin Afrika

Samfurin maganin kwaya cutar HIV

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, Dakta Ibrahim Jidda, kwararren likita kan kwayar cutar HIV mai karya garkuwar jiki, a asibitin koyarwa da ke jihar Taraba, ya yi karin hasken cewa samfurin maganin na DTG ba wai sabo bane da ya banbanta da wanda aka fi sani a baya, illa sake fasalta shi da aka yi a yanzu.

Sai dai kuma Dr Jidda ya ja hankalin hukumomin Najeriya, kan sa ido wajen rigakafin duk wani yunkuri na bata gari, na yin amfani rahusar farashin maganin, domin kirkirar na jabu a kasar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan
NAIJ.com
Mailfire view pixel