Jama’a sun hurowa Gwamna El-Rufai wuta bayan yayi magana biyu

Jama’a sun hurowa Gwamna El-Rufai wuta bayan yayi magana biyu

– Gwamna El-Rufai yayi magana game da yi wa tsarin kasa garambawul

– El-Rufai yayi kaca-kaca da masu kira ayi wa Najeriya kwaskwarima

– Sai dai kuma a baya an taba samun sa yana irin wannan magana

El-Rufai ya soki masu kirar ayi garambawul ga tsarin Najeriya. Amma fa a baya an taba kama sa yana wannan kira. Hakan ta sa wasu su kace Gwamnan yayi magana biyu.

Jama’a sun hurowa Gwamna El-Rufai wuta bayan yayi magana biyu

Gwamnan Jihar Kaduna Mallam El-Rufai

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmed El-Rufai ya soki masu kirar ayi garambawul ga tsarin mulkin Najeriya inda ma ya kira wadanda ke wannan maganar da cewa sun samu wuri ne kurum.

KU KARANTA: Jama'a sun yi ca a kan Gwamna Fayose

Jama’a sun hurowa Gwamna El-Rufai wuta bayan yayi magana biyu

Gwamna El-Rufai tare da Farfesa Osinbajo

Sai dai a baya NAIJ.com ta samu tabbacin cewa Gwamnan da bakin sa ya taba yin irin wannan kira. Sai dai wannan karo Gwamnan yace tuni har an fara ragewa Shugaban kasa karfi ta hanyar wasu zama da dama da ake yi.

Shi kuma Tsohon Shugaban kasar Najeriya Cif Olusegun Obasanjo yayi magana a wani taro a Garin Kigali inda yayi kira ga Shugabannin kasashen Afrika na Kungiyar ECOWAS su kara hada kai domin Yankin ya cigaba.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko Najeriya za ta kara dawowa yadda aka san ta?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel