Mutanen Taraba 3000 na gudun hijira a Kamaru

Mutanen Taraba 3000 na gudun hijira a Kamaru

- Dubban mutane daga jihar Taraba sunyi gudun hijira zuwa jamhuriyyar Kamaru, inda anan aka basu masauki

- Mafi yawa daga cikin yan gudun hijran Fulani makiyaya ne wadanda suka hada da mata da kananan yara

- Kimanin mutane 3,000 ne suka yi gudun hijira zuwa garuwa irin su Mayo-Darle, a Lardin Adamawan

Rahotanni dake zuwa mana sun nuna cewa dubban mutane daga jihar Taraba sunyi gudun hijira zuwa jamhuriyyar Kamaru, inda anan aka basu masauki.

Mafi yawa daga cikin yan gudun hijran Fulani makiyaya ne wadanda suka hada da mata da kananan yara da suka tsere daga jihar ta Taraba sakamakon rikicin da ya shiga tsakaninsu da yan kabilar Mambila.

Bisa ga rahoton, kimanin mutane 3,000 ne suka yi gudun hijira zuwa garuwa irin su Mayo-Darle, a Lardin Adamawan, inda aka basu masauki a makarantun boko.

KU KARANTA KUMA: Bamu iya cinye abin da muke nomawa - Minista Ogbeh

Mutanen Taraba 3000 na gudun hijira a Kamaru

Mutanen Taraba 3000 na gudun hijira a Kamaru

Har ila yau rahoto daga Mayo-Darle na cewa ana ci gaba da samun sababbin yan gudun hijira daga jihar Taraba a kokarinsu na neman mafaka.

Haka kuma akwai rahoto dake cewa akwai wasu dumbin 'yan gudun hijirar da ke samun kulawa a asibitin Fanso sakamakon raunukan da suka ji.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyo na NAIJ.com a kasa:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel