Bamu iya cinye abin da muke nomawa - Minista Ogbeh

Bamu iya cinye abin da muke nomawa - Minista Ogbeh

- Muna noma abincin da yafi karfin bakin mu a Najeriya

- Siyar da doyar mu a kasuwannin duniya zai samar ma Najeriya Karin kudin shiga

- Sannan kuma zai rage asarar da mukeyi dalilin rashin wurin ajiya

Ministan noma da raya karkara Mista Audu Ogbeh yace Najeriya tana noma abincin da yafi karfin bakin mutanen kasar.

Ya cigaba da cewa galibin kayan abincin da ake noma suna lalacewa ne saboda rashin dabarun ajiya a kasar. Ya fadi wannan maganan ne a taron kaddamar da fita da doya don sayarwa a kasuwannin duniya.

Ya koka da cewa fitar da abincin zuwa kasuwannin duniya yana daya daga cikin hanyoyin da za’a bi domin rage asara da banar abincin da ake nomawa.

KU KARANTA KUMA: Wani dan Najeriya mai basira ya kera motoci a jihar Kebbi

Bamu iya cinye abin da muke nomawa - Minista Ogbeh

Bamu iya cinye abin da muke nomawa - Minista Ogbeh

Ya kuma kara jadada mahimancin yadda siyar da doyar a kasuwanin duniya zai bunkasa kudin shiga da Najeriya ke samu.

Bamu da karancin doya, sabuwar doya zata shigo kasuwa nan da makonni kadan. Tsohuwar doyar har yanzu tana kasuwa kuma idan sabon ya fito, mutane zasu dena siyar tsohuwar doyan.

“A zahiri muna noma abin da yafi karfin bakin mu a Najeriya, kashi talatin zuwa arba’in na abincin da muke nomawa asarar shi akeyi saboda rashin wurin ajiya.” Inji Minista Ogbeh

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel