Rashin lafiyar Buhari: Abun da shugaban APC Oyegun ya ce

Rashin lafiyar Buhari: Abun da shugaban APC Oyegun ya ce

- Shugaban jam’iyyar APC ta kasa, John Oyegun ya kaddamar da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na samun lafiya sosai cikin sauri

- Wannan ya biyo bayan zargin da gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya yi na cewa shugaban kasar bai san inda kansa ya ke ba

- Ya bayyana furucin gwamnan a matsayin abun takaici

A ranar Alhamis 29 ga watan Yuni, Shugaban jam’iyyar APC ta kasa, John Oyegun ya kaddamar da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na samun lafiya sosai cikin sauri.

Oyegun ya kaddamar da hakan ne yayinda yake karyata zargin gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose da ya ce Buhari bai san inda kansa yake ba.

Da aka nuno shi a Channels television, Oyegun ya nace kan cewa lallai Buhari baya cikin mawuyacin hali kamar yadda Fayose ya yi zargi.

KU KARANTA KUMA: Kacaniya ta kaure tsakanin Ýan banga da Matasa, anyi ƙone ƙone (HOTUNA)

Rashin lafiyar Buhari: Abun da shugaban APC Oyegun ya ce

Oyegun ya ce shugaba Buhari na samun sauki sosai

A cewar shugaban na jam’iyyar APC, furucin Fayose ya kasance “abun takaici.”

Ya ce: “Idan gwamnan jihar Ekiti ya yi magana kawai ka kale shi ka ci gaba da abun da kake yi.

“Mu ba likitocin sa bane amma rahotanni da muka samu masu kyau ne sosai.

"Furucin Fayose abun takaici ne sosai. Bai kamata ba. Babu wanda zai yi ma kansa fatan haka ko a kan kasa amma dai yana samun lafiya sosai.”

Idan zaku tuna NAIJ.com ta rahoto cewa shugaban kasa Buhari ya bar kasar a ranar 7 ga watan Mayu domin ci gaba da jinya a birnin Landan, wanda har yanzu ba’a bayyana ma ‘yan Najeriya abun da ke damun sa ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel