Kogi: Akalla motoci 10 suka kone kurmus a hadarurruka da ta auku a Kogi

Kogi: Akalla motoci 10 suka kone kurmus a hadarurruka da ta auku a Kogi

- Hukumar FRSC ta ce mutane 4 ne suka mutu da kuma motoci 10 sun kone a hadarurruka 4 da ta auku a jihar Kogi

- Babban kwamandan hukumar ya ce hadarurruka guda hudun sun faru ne a Kabba, Okene, Ankpa, da kuma Koton Karfe

- Martins ya ce wasu mutane 4 kuma sun ji rauni mai tsanani a hadarurrukan

Hukumar FRSC ta bayyana cewa a ranar Alhamis, 29 ga watan Yuni wasu mutane biyu suka mutu, kuma motoci 10 suka kone a hadarurruka 4 da suka faru a sassa daban daban na jihar Kogi tsakanin ranar 23 da 28 ga watan Yuni.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, babban kwamandan hukumar na jihar, Mista Olusegun Martins ya sanar da haka ga manema labarai a Lokoja, ya ce hadarurruka guda hudun sun faru ne a Kabba, Okene, Ankpa, da kuma Koton Karfe.

A cewar kwamandan, wasu mutane 4 kuma sun ji raunin mai tsanani a hadarurrukan.

Kogi: Akalla motoci 10 suka kone kurmus a hadarurruka da ta auku a Kogi

Wasu daga motoci 10 da suka kone kurmus a Kogi

Martins ya ce motoci 10 suka kone gaba daya a yankin gidan mam na Total da ke Okene a ranar 23 ga watan Yuni a lokacin da wata babban motar man fetur ya kama da wuta.

KU KARANTA: Kacaniya ta kaure tsakanin Ýan banga da Matasa, anyi ƙone ƙone (HOTUNA)

Kwamandan ya ce kwanan nan an samu karuwar yawan manyan motoci da suke bin hanyar Okene-Lokoja-Abuja sanadiyar rushewar gadan Mokwa da ke jihar Neja.

Kwamandan ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gyara gadan kafin wani bikin murnar sallah domin rage cinkoso a kan hanyan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel