Rikici tsakanin jikan Sardauna da jigon APC tayi fallatsa har fadar Sarkin Musulmi

Rikici tsakanin jikan Sardauna da jigon APC tayi fallatsa har fadar Sarkin Musulmi

Rashin jituwa dake tsakanin magajin garin Sakkwato,kuma jikan Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato, Alhaji Hassan Danbaba da kuma mataimakin shugaban jam’iyyar APC Alhaji Inuwa Abdulkadir yayi kamari.

Rikicin nasu ya samo asali ne tun lokacin da gwamnan jihar Sakkwato ya aika ma Sarkin Musulmi da a nada Inuwa a matsayin Marafan Sakkwato, wanda shi kuma Danbaba yace bai kamata a nada shi ba saboda duk iyayensa bayi ne.

KU KARANTA: An ci Boko Haram da yaki? Shekau ya karaya a sabon bidiyon daya fitar

A baya, NAIJ.com ta kawo rahoto, inda wata kotu ta bada umarnin a kawo mata Danbaba kota halin kaka, sakamakon rashin gurfana a gabanta, bayan kararsa da Inuwa Abdulkadir ya shigar.

Rikici tsakanin jikan Sardauna da jigon APC tayi fallatsa har fadar Sarkin Musulmi

Magajin Gari da Sultan

Sakamakon rikicin da yaki ci, yaki cinyewa ne yasa mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya shiga tsakaninsu da nufin kawo sulhu, inda kowa ya fadi korafinsa, daga nan Sarkin ya sanard a sulhunta mutanen biyu.

Sai dai bayan wannan zaman sulhu ne, sai Inuwa Abdulkadir ya kawo wata takarda da nufin Sarkin Musulmi ya umarci Danbaba daya sa hannu akanta, domin ya zama shaida cewa lallai an yi sulhu, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Rikici tsakanin jikan Sardauna da jigon APC tayi fallatsa har fadar Sarkin Musulmi

Inuwa

Sai dai batutuwan da takardar ta kumsa basu yi ma Danbaba dadi ba, inda yayi watsi da bukatar Inuwa da Sultan, hakan ya bata ma Sarkin rai, inda ya zargi Danbaba da cin kudin bashin Paris, nan take shi kuma ya mayar masa martani cewa ai ba satar su yayi ba, shi yasa EFCC basu kama ni ba.

Daga nan ne ya fita daga fadar, sa’annan yayi murabus daga mukamin nasa na magajin gari, kuma ya aiko ma fadar sarkin musulmi da dukkanin motocin su da sauran kayayyakinsu, sai dai ance Sultan ya mayar masa dasu, inji Daily Nigerian.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin Najeriya tamu ce duka?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel