Boko Haram ta kai hari a sansani yan gudun hijira dake ƙasar Nijar

Boko Haram ta kai hari a sansani yan gudun hijira dake ƙasar Nijar

- Maharan Boko Haram ýan ƙunar baƙin wake sun kai hari sansanin ýan gudun hijira a Nijar

- Sama da mutane goma sha uku sun samu raunuka daban daban

Sansanin yan gudun hijira yan Najeriya dake jihar Diffa na kasar Nijar ya gamu da hare hare yan kunar bakin wake a ranar Laraba 28 ga watan Yuni, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Harin yayi sanadiyyar mutuwar akalla mutane hudu, tare da jikkata mutane 13. Majiyar NAIJ.com ta jiyo majiya da dama suna bayyana cewar yan kunar bakin wake hudu ne suka nufo sansanin, maza 2 mata 2.

KU KARANTA: Anyi ma Barack Obama babban tarba a ƙasar Indonesiya inda yaje yawon hutu (HOTUNA)

Sai dai matan ne kadai suka shigo sansanin, yan mazan basu shiga ba, sa’annan da suka fahimci matan sun tayar da bama bamansu, sai suka ruga zuwa tafkin Chadi.

Boko Haram ta kai hari a sansani yan gudun hijira dake ƙasar Nijar

Sojojin kasar Nijar

A yanzu dai an karfafa tsaro a sansanin yan gudun hijiran don magance sake mamaituwar lamarin.

Boko Haram ta kai hari a sansani yan gudun hijira dake ƙasar Nijar

Harin kunar bakin wake

A yan kwanakin nan an samu karuwar yawaitan hare haren kunar bakin wake daga kungiyar Boko Haram, inda ko a makon data gabata sai da aka samu irin wannan hari sau 7 a jami’ar Maiduguri dake jihar Borno.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel