Kacaniya ta kaure tsakanin Ýan banga da Matasa, anyi ƙone ƙone (HOTUNA)

Kacaniya ta kaure tsakanin Ýan banga da Matasa, anyi ƙone ƙone (HOTUNA)

Wani tarzoma daya balle a garin Kontagora na jihar Neja yayi sanadiyyar mutuwar mutane uku, ciki har da karamin yaro, yayin da wasu mutane 2, mace da namiji suke jinya a yanzu haka.

Jaridar Rariya ta ruwaito wannan mummunan aika aika ya faru ne a ranar Alhamis 29 ga watan Yuni, kuma ya samo asali ne sakamakon rasuwar wani matashi da yan bangan garin Kontagora suka kama, suka lakada masa dan banzan duka tun a watan Azumi.

KU KARANTA: 2019: Kwankwasawan jihar Katsina sun yi kira da babban murya ga Sanata Kwankwaso

Tun daga wannan lokaci ne fa matashin ya fara rashin lafiya, kuma mahukunta basu dauki hukunci akan yan bangan ba, har sai jiya da Allah yayi ma wannan yaron rasuwa sakamakon jinyar da yayi ta fama da shi, wanda wannan ne ya harzuka matasan garin, suka far ma ofishin yana bangan.

Kacaniya ta kaure tsakanin Ýan banga da Matasa, anyi ƙone ƙone (HOTUNA)

Ofishin

Majiyar NAIJ.com ta bayyana cewar anyi dauki ba dadi, an kai ruwa an kai mari tsakanin matasan yankin da yan bangan, daga karshe dai matasan sun banka ma ofishin yan bangan wuta, inda yak one kurmus.

Kacaniya ta kaure tsakanin Ýan banga da Matasa, anyi ƙone ƙone (HOTUNA)

Ofishin

Sai dai suma yan bangan fa sun yi harbe harbe da bindigun su, wanda hakan ya samu wani mutum guda, nan take ya mutu, yayin da mutane biyu kuma suka samu raunuka daga harbe harben, sai wani yaro da ake tunanin yamutsi ne yayi ajalinsa.

Kacaniya ta kaure tsakanin Ýan banga da Matasa, anyi ƙone ƙone (HOTUNA)

Ofishin

Dama dai jama’an garin Kontagora sun dade suna korafi kan yadda yan bangan garin ke gudanar da aiknsu, inda suka ce sau dayawa suna wuce gona da makadi, inda abu kadan sai kaga suna cin mutuncin jama’a.

Kacaniya ta kaure tsakanin Ýan banga da Matasa, anyi ƙone ƙone (HOTUNA)

Yan gari

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel