Kotu ta yassare ma iyaye daman kashe ýaýansu jarirai a wata ƙasa, Karanta

Kotu ta yassare ma iyaye daman kashe ýaýansu jarirai a wata ƙasa, Karanta

Wata kotun yancin dan Adam ta hadaddiyar kasashen nahiyar turai ta yanke wani hukunci mai daure kai, inda ta bada iyaye daman su kyale yaronsu jariri ko jaririya su mutu muddin basu da lafiya.

Kotun ta bada wannan dama ne sakamakon wani shari’a dake gabanta inda wasu iyaye Chris Gard da Connie Yates suka shigar da kara biyo bayan wani irin ciwon sinadarin halittar mutum data addabi jaririnsu.

KU KARANTA: Ina masu motoci? Hamid Ali yayi bayani kan hanyoyin tantance takardun mota na bogi

Iyayen jaririn sun koka kan cewa sun yi iya bakin kokarinsu, amma cutar taki ci, taki cinyewa, kuma a yanzu haka, jaririn na nan, rai fakwai, mutu fakwai. An tabbatar da cewa jarirai masu dauke da irin cutar da jaririn ke fama dashi su 16 ne kacal a duniya.

Kotu ta yassare ma iyaye daman kashe ýaýansu jarirai a wata ƙasa, Karanta

Jariri mara lafiya

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito iyayen yaron sun bukaci kotu data tabbatar musu da ko suna da daman kwale yaron har ya mutu, ko kuwa lallai sai sun cigaba da kulawa da shi?

Don haka ne kotun a ranar 27 ga watan Yuni ta yanke hukuncin baiwa iyayen jaririn damar kashe shi, sakamakon yana fuskantar tsananin ciwo da cutarwa, musamman yadda babu maganin cutar dake damunsa.

Majiyar NAIJ.com ta bayyana cewar an tara ma iyayen jaririn sama da pan miliyan 1.3 domin baiwa yaron kulawa, amma biyo bayan wannan hukuncina kotu, suna tunanin idan yaron ya mutu zasu biya kudin kulawarsa tare da tallafa ma sauran jarirai masu dauke da irin ciwon shi.

“Domin bama son wani jariri ya fuskanci wahala kamar yadda yaron mu ya fuskanta.” Inji iyayen.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Hanyoyin magance kamuwa da cutar Typhoid, Kalla:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel