Yobe: Gwamnatin Yobe ta kaddamar da gyara gidajen da Boko Haram ta rushe

Yobe: Gwamnatin Yobe ta kaddamar da gyara gidajen da Boko Haram ta rushe

- Gwamnatin jihar Yobe ta fara jare jaren ofisoshin gwamnati da gidajen da kungiyar Boko Haram ta rusa a jihar

- Gwamnatin jihar ta ce yanzu haka ta bada kwangila miliyan 105 daga cikin tsarin

- Shugaban ma’aikatan jihar ya ce gwamna Gaidam na jajirce wajen biyan albashin ma'aikata da kuma alawus alawus

Gwamnatin jihar Yobe ta kaddamar da gina ofishin gwamnatin jihar da kuma wasu gine-ginen da kungiyar Boko Haram suka rushe a fadin jihar.

NAIJ.com ta ruwaito cewa, shugaban ma’aikatan jihar, Alhaji Sale Abubakar, ya bayyana haka a ranar Alhamis, 29 ga watan yuni a garin Damaturu yayin da yake duba aikin gine-gine a kan wasu daga cikin tsarin.

Abubakar ya ce gwamnati jihar ta bayar da kwangila kudi naira miliyan 105 tsarin farko na sake gine-ginen.

Yobe: Gwamnatin Yobe ta kaddamar da gyara gidajen da Boko Haram ta rushe

Gwamnan jihar Yobe Ibrahin Gaidam

KU KARANTA: Kamaru ta dawo da wasu ‘yan Najeriya 887 zuwa gida

Ya ce gwamna Gaidam na jajirce wajen biyan albashin ma'aikata da kuma alawus na ma'aikatan a cikin lokaci.

Saleh ya yi alkawarin cewa gwamnati jihar zata ci gaba da samar da yanayin moriyan aiki ga ma'aikatan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan
NAIJ.com
Mailfire view pixel